✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama barauniyar jariri dan wata daya

Wata mata mai shekara 21 ta faɗa komar ’yan sanda sakamakon zargin ta da sace wani jinjiri dan wata guda da haihuwa.  Kakakin rundunar ’yan…

Wata mata mai shekara 21 ta faɗa komar ’yan sanda sakamakon zargin ta da sace wani jinjiri dan wata guda da haihuwa. 

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da kama matar a ranar Laraba.

Ya ce mahaifiyar jaririn ce ta kai rahoto a ofishin ’yan sanda da ke  yankin Elere a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mai jegon ta ce an sace dan nata ne da misalin karfe 7 na safiyar Asabar yayin da take barci.

Hundeyin ya ce wacce ake zargin ta je coci domin shaida wa jama’arta cewa ta haihu.

Ya ce an gano wadda ake zargin ne a unguwar Agbotikuyo da ke Agege an kuma yi nasarar kwato jaririn daga hannunta.