✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai saurayi kurkuku kan cizon mace a lebe

Matashi ya gantsara wa wata mata cizo a yayin wata takaddama

Kotu ta tsare wani matashi a gidan yari kan zargin cizon wata mata a lebe.

Kotun Majiatare da ke zamanta a yankin Maponta ba da umarnin tsare matashin mai shekaru 27 a  gidan yari na Agodi da ke jihar Oyo.

An gurfanar da matashin ne gaban Mai Shari’a Misis O.O. Latunji, kan cizon da ya gantsara wa matar a yayin wata takaddama.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Oluseye Akinola, ya shaida wa alkali cewa an kama wanda ake zargin ne bayan da ya ciji matar a lebenta  a ranar Litinin.

Bayan sauraron karar alkali ta ba da umarnin tsare matashin a gidan yari ta kuma dage shari’ar zuwa ranar 3vga watan Yuni, 2024.