✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi sun duro daga bene ana tsakar tuhumarsu a kotu

An garzaya da su zuwa Asibitin don kula da lafiyarsu inda za a ci gaba da tsare su a gidan yari.

Wasu mutum biyu da ke zargi da laifin fashi da makami a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo sun yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar duro wa daga wani ginin bene mai hawa biyu a kotun da ke sauraron tuhumar da ake yi masu.

Mai gabatar da ƙara a Kotun Majastare ta Iyaganku da ke Ibadan, Sufeton ‘yan sanda Femi Omilana ya ce, tun cikin shekarar 2023 kotu ta bayar da umarnin tsare waɗanda ake zargin.

Ya bayyana ana tuhumar waɗannan mutane — Damilare Adeniran da abokinsa Victor — tare da wasu uku da laifin yin amfani da bindigogi da wasu makamai wajen yi wa jama’a fashi.

Ya ce, waɗannan ‘yan fashi sun kuɓuce daga hannun jami’an tsaro a cikin Kotun ne suka yi kasadar tsallaka tagar Kotun da suka duro ƙasa inda suka samu munanan raunuka a sassan jikinsu.

Sufeto Omilana ya ce ‘yan fashin sun duro ƙasa ne a daidai lokacin da Alkali G. Oladele na Kotun Majastare yake sauraron ƙarar da ake tuhumarsu a ranar Laraba.

Ya ce an garzaya da su zuwa Asibitin don kula da lafiyarsu inda za a ci gaba da tsare su a gidajen yari.

Alƙalin Kotun ya ɗage ci gaba da sauraron tuhumar da ake yi musu zuwa ranar 8 ga watan Yuli mai zuwa.