✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa dillalan ƙwayoyi hukuncin ɗaurin shekaru 95 

NDLEA ce ta kama dillalan tare da gurfanar da su s kotu, kafin daga bisani aka yanke musu hukunci.

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 a gidan yari.

Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas a bara, yana ƙoƙarin shigowa da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kusan kilogram 20, wadda kuɗinta ya kai biliyan 46.

Sauran da aka kama sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (wanda aka fi sani da Don), da kuma Zidon Zurga.

Ko da yake, ba wannan ne karo na farko da aka kama Ogbuji ba.

A baya, an kama shi watanni 16 da suka gabata bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Hukuncin Da Kotu Ta Yanke

Baya ga hukuncin ɗaurin shekaru 95 ko tarar Naira miliyan 25, kotu ta kuma umarci a ƙwace motocin da aka yi amfani da su wajen safarar ƙwayoyin.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba da hukuncin kotu da kuma ƙoƙarin jami’an NDLEA wajen kama masu safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.