✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbi dalibai 3 an sace wata a Kwalejin IMAP da ke Nasarawa

Dalibar da aka sace tana ’yar aji biyu ce a matakin difloma a fannin Kimiyyar Dakin Gwaje-gwaje.

’Yan bindiga sun harbi dalibai uku sannan suka sace wata daliba a Kwalejin Kimiyya da  Kere-Kere ta Isa Mustapha Agwai (IMAP) da ke garin Lafia a Jihar Nasarawa.

Rahotanni daga kwalejin sun ce dalibar da aka sace ’yar aji biyu ce a matakin difloma a fannin Kimiyyar Dakin Gwaje-gwaje.

Shaidu sun ce an ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 8 na dare ranar Litinin.

Kwana biyu ke nan da makamancin haka ta faru a Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, inda ’yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai mata kimanin 24 daga dakunan kwanansu a unguwar Sabon Gida da ke makwabtaka da jami’ar.

Maharan na Zamfara sun sace wasu maza biyu ’yan unguwar sannan suka kutsa cikin harabar jami’ar suka hada da wasu masu aikin walda su tara.

Daga bisani dai sojoji sun yi artabu da su, har suka yi nasarar ceto 10 daga cikin mutanen, a yayin da ake ci gaba da kokarin ganin ragowar ma sun kubuta.

%d bloggers like this: