✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka ceto 10 daga cin daliban jami’a da aka sace a Zamfara

Sojoji sun kubutar da 10 daga cikin daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga Jami'ar tararyya da ke Gusau a Jihar Zamfara.

Sojoji sun yi kubutar da 10 daga cikin mutum sama da 30 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga Jami’ar Ttararyya da ke Gusau a Jihar Zamfara.

Sojoji da mazauna yankin Sabon Gida da ke daura da Jami’ar, inda lamarin ya faru, sun tabbatar da hakan tare da NUNA kwarin gwiwarsu cewa sojoji za su yi nasara a aikin da suke ci gaba da yi na ceto ragowar wadanda ke hannun ’yan bindigar.

Yadda aka sace daliban

A ranar Juma’a ne ’yan bindiga suka kutsa unguwar Sabon Gida suka fasa wasu gidajen kwanan dalibai uku, suka tisa keyar dalibai mata akalla 24, da wasu maza mazauna unguwar  guda biyu.

Daga nan maharan suka kutsa cikin jami’ar harabar inda suka yi awon gaba da wasu masu aikin walda su tara.

Harin dai shi ne na farko da aka yi garkuwa da dalibai tun bayan hawa mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya yi alkwarin magance matsalar ysaro da ta addabi Najeriya.

Yadda aka ceto daliban FUGUS

Sojojin da ke yankin sun yi ba ta-kashi-da  maharan, inda suka yi nasarar ceto shida daga cikin dalaban, daya daga cikin  masu aikin waldar kuma ya tsere a yayin musayar wutar.

A ranar Litinin kuma sojoji suka yi wa ’yan bindigar kwanton bauna a Babban Kauye kusa da garin Tsafe, a cewar majiyoyinmu da suka ce ba a ba su izinin magana ba game da aikin ceton.

Ba kasafai hukumomin Jihar  Zamfara ke magana kan adadin wadanda aka yi garkuwa su ba, amma wata majiyar soji ta ce, “sojoji sun kubutar da mutum 10, ciki har da dalibai mata bakwai, a musayar wuta da ta sa ’yan ta’ddan tserewa su bar su.

“Amma an ci gaba da aikin ganin an ceto wadanda aka sace,” in ji sojan.

Wani ma’aikacin jami’ar ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an ceto 10 daga cikin wadanda aka sacen.

Shi ma wani uban kasa a yankin ya tabbatar da hakan, inda ya kara da cewa kokarin sojojin ya ba su kwarin gwiwar cewar za a ceto ragowar matanen.

Garkuwa da mutane a Zamfara

Zamfara na daga cikin johihin Arewacin Najeriya da ’yan bindiga suka addaba, inda suke kai wa kauyuka hare-hare su kashe na kashewa su sace na sacewa su kona gidaje da shaguna su kwashi kadarori.

Masu wannan aika-aika sun kafa sansanonin a cikin dazukan da suka ratsa ta jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da kuma Neja.

A watan Fabrairun 2021 ’yan bindiga suka kai hari a wata makarantar sakandaren kwana da ke garin Jangebe a Jihar Zamfara, suka sace dalibai sama da 300, kafin daga baya su sako su.