Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta haramta duk wani nau’i na kilisa da hawan angonci da taron majalisi ba tare da izini ba.
Wannan mataki ya biyo bayan yadda wadansu bata-gari suke amfani da wadannan wurare suna aikata manyan laifuka ne, a cewar rundunar ‘yan sandan.
- Shinkafa ta yi tsadar da ba a taɓa gani ba cikin shekara 15 a duniya — FOA
- Uwa ta ƙona ɗanta da ruwan zafi kan zargin neman mata
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa ta hoton bidiyo da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya gabatar a shafin Facebook.
Kiyawa ya nado Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano Mohammed Usaini Gumel yana cewa, an dauki matakin ne saboda ganin yadda tabarbarewar al’amuran tsaro ke son dawowa a birnin na Kano.
“Mun lura cewa matasa na karya doka tare da amfani da wasu damarmaki don aikata laifuka,” in ji CP Gumel.
Ya ci gaba da cewa, “Bincike ya nuna wa ‘yan sanda cewa hawan kilisa da hawan angonci da taron majalisi su ne wuraren da ake samun rashin jituwa tsakanin matasa, kuma ake aikata laifuka.”
A baya ma hukumomi sun taba saka dokar hana wadannan al’amura da suka shafi kilisa, kamar yadda kwamishinan ya tabbatar, sai dai da alama wancan hanin bai rage komai ba, a cewar masu sa-ido kan al’a’mura a jihar.
“Don haka a ranar 7 ga watan Satumba, mun yi taro da ‘yan majalisar Sarkin Kano, da suke lura da harkokin hawan dawaki, inda muka zartar da cewa duk wanda zai hau doki don yin angonci ko kilisa ko harkar taron majalisi, to akwai ka’idoji da aka tanadar cewar sai masu son yi sun nemi izini kafin yi.
“Saboda gudun kar bata-gari su shiga cikinsu su yi amfani da damar wadannan tarukan su aikata wani abu na cutar da al’umma,” in ji Kwamishina Gumel.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce hukumomi sun zartar da cewa daga yanzu ‘yan sanda za su fita su sa ido, don ganin duk wanda ya karya dokar ya fuskanci hukunci.
“Kuma cikin ka’idojin dole ya kasance masu hawan dokin su kasance cikin shiga ta kamala, ba wai a hau doki da gajeren wando ba ko sa hula wacce da gani ta neman fada ce.”
Ya koka cewa a wajen majalisi kuma wasu kan kai ruwan sha, irin yadda ake yi a al’adance, amma sai su zuba kwaya a ciki don mutane su sha su bugu.
“To fa duk wanda aka kama da aikata hakan za a gurfanar da su a gaban kuliya don amsa laifukansu,” CP Gumel ya fada.
Tayar da hargitsi a wajen kilisa
Ga duk wanda ya san yadda al’amura suke gudana a birnin Kano, da abin da ya shafi kilisa da zaman majalisi, ya san irin ta’azzara rashin tsaro da ke faruwa, in ji wani dan jarida kuma mazaunin cikin birnin, Umar Dandago.
“Akwai lokacin da wani rikici na kilisa ya kusa ritsawa da ni sanda na je wata sabga a unguwar Race Course da ake cewa Filin Sukuwa, inda wasu ‘yan daba suka tayar da hargitsi a wajen kilisar aka yi kare-jini biri-jini.”
Dandago ya shaida wa TRT cewa a unguwannin cikin birnin Kano yawanci duk Juma’a ko Asabar sai an hada kilisa, ko ta nishadi ko ta angonci, amma ba a faye wanyewa lafiya ba.
Ya kara da cewa, “Har kashe-kashe ana samu saboda fadan da ake tayarwa a wuraren, ko kuma a saki dawakai a cikin lunguna, su bi ta kan mutane har a samu mutuwa, ko su dinga razana mata da yara.”
An sha yada bidiyoyi a shafukan sada zumunta da ke nuna masu kilisar na bi ta kan mutane tare da buge wanda bai ji ba bai gani ba, ko kuma su da kansu su fado daga kan dawakan, su ji munanan raunuka ko su rasa rai.
A wuraren majalisi wadanda akan taru ana wake-waken bege, ana samun hatsaniya ta ‘yan daba, ko ta ‘yan shaye-shaye, in ji dan jaridar.
A ganinsa, wannan sabon hanin zai iya yin tasiri ne kawai idan har hukumomi suka tilasta bin dokar, da nuna ba sani ba sabo don hukunta duk wanda aka kama da laifi, tare da tabbatar da hukunci kan masu aikatawa.
“Ta haka ne kawai zaman lafiya da tabbatar da tsaro zai inganta a wannan jiha tamu,” ya ce.
Ita ma rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga al’umma da su ba ta hadin-kai “kamar yadda aka saba, don samun zaman lafiya da kyautatuwar al’umma.”