✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shinkafa ta yi tsadar da ba a taɓa gani ba cikin shekara 15 a duniya — FOA

FAO ya ce hakan ba ya rasa nasaba da haramta fitar da shinkafar da Indiya ta yi.

Kungiyar Abinci da Noma ta Duniya (FAO) ta ce farashin shinkafa a duniya ya kai matsayin da bai taɓa kaiwa ba cikin shekara 15 a watan Agusta.

Hauhawar farashin ya faru ne bayan Indiya, wadda ta fi kowa fitar da shinkafar a duniya, ta haramta sayar da shinkafar zuwa wasu ƙasashe.

A yayin da farashin kayan abinci ya sauka a watan Agusta, farashin shinkafa ya ƙaru da kashi 9.8 idan aka kwatanta da watan Yuli.

FAO ya ce hakan ba ya rasa nasaba da haramta fitar da shinkafar da Indiya ta yi.

Shinkafa ce babban abincin da aka fi ci a duniya, kuma farashinta ya tashi tun bayan ɓullar annobar Coronavirus da ɓarkewar yaƙin Ukraine.

A watan Yuli ne Indiya ta sanar da haramta fitar da shinkafar da ba basmati ba, wadda ta kai kusan kashi ɗaya cikin huɗu na adadin shinkafar da ƙasar ke fitarwa

Ma’aikatar abinci ta ƙasar ta ce an ɗauki matakin ne domin magance ƙarancin shinkafar da saukar da farashinta a cikin ƙasar.