✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hada taransifomar lantarki 20 na Kamfanin Siemens a Najeriya —FGN Power

Gwamnatin Tarayya ta ce kashi 80 cikin 100 na kayan aikin samar da wutar lantarki da ta kulla yarjejeniya da kamfanin Siemens sun na hannunta

Gwamnatin Tarayya ta ce kashi 80 cikin 100 na kayan aikin samar da wutar lantarki da ta kulla yarjejeniya da kamfanin Siemens na kasar Jamus sun shigo hannunta.

Kamfanin samar da wutar lantarki na FGN Powar ya ce kaya da suka shiga hannunta sun hada da taransfoma 10 da tashoshi na lantarki na tafi da gidanka guda 10 kuma ya fara amfani da su a kashin farko na shirin samar da wutar lantarki ta hannun kamfanin Siemens (PPI).

Aminiya ta ruwaito a kwanan baya cewa an samu tsaki a 2021 a kan aikin da aka farko da niyyar kara karfin wutar lantarkin Najeriya da megawatt 2,000 zuwa megawatt 7,000.

Amma sanarwar da Kamfanin ya fitar ranar Laraba, ya ce har yanzu kashin farko na aikin “na ci gaba da gudana kuma ya sami gagarumar nasara,” kasancewar aikin gwaji.

Ya ci gaba da cewa: “Kamfanin ya karbi kusan kashi 80 cikin 100 na kayan aikin gwajin, kuma tura su zuwa wurare masu mahimmanci a fadin kasar don inganta karfin samar da wutar lantarki.”

Wasu daga cikin wuraren sun hada da Kwanar Dangora da Birnin Kebbi da Potiskum da Apo da Ajah da Okene da Lake Nike da Maryland da Omouaran da Ojo da Amukpe da Ihovbor da dai sauransu.

Da yake tsokaci, Manajan Daraktan Kamfanin FGN Power, Mista Kenny Anuwe, ya ce idan aka kammala kashi na biu na aikin karin wutar zai karu zuwa megawatts 11,000, kashi na uku kuma zai kai shi zuwa 25,000MW.

“Nasarar aiwatar da kashi na 1 zai kai ga samar da karin 2000MW da kuma sabbin hanyoyin sadarwa miliyan 2 zuwa tashar wutar lantarki ta kasa hadi da horar da injiniyoyi sama da 5,000 don gudanar da cibiyoyin, da kuma inganta wutar lantarki ga miliyoyin ’yan Najeriya,” in ji Anuwe .

Ya zargi annobar COVID-19 da kawo koma baya ga kamfanin Siemens wajen kera wadatattan kayan da ake bukata masana’antu.

Anuwe ya ce: “An yi ta yada cewa an hada na’urar taransifoma mai karfin 60MVA Siemens a tashar Apo Transmission, Abuja, kuma hakan ya isa shaida cewa aikin yana tafiya kuma zai ci gaba da samar da ingantacciyar wutar lantarki da fadada tadomin amfanin al’umma da tattalin arzikin Najeriya.