✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Arewa ke jefa yankin cikin jahilci —Ministan Ilimi

Adamu Adamu ya ce duk ’yan Arewa na tutiya da addinin Musulunci wanda ke karfafa neman ilimi, amma su ke yi wa harkar neman ilimi…

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya zargi ’yan Arewacin Najeriya da zama musabbabin yaduwar jahilci a yankin.

Ministan ya ce duk da cewa ’yan Arewa na bugun kirji da addinin Musulunci wanda ke karfafa neman ilimi, amma kuma su ke yi wa harkar neman ilimi manakisa.

Ya ce, idan ba haka ba, jami’o’i biyu na farko a duniya mata Musulmi ne suka kafa su, amma kuma wasu a Arewa na “fakewa da Musulunci suna hana mata fita neman ilimi.”

Ministan ya yi wannan furuci ne a taron kaddamar da manhajar karatun jami’o’i da wani littafi a kansa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta gudanar a Abuja.

Ya jinjina wa NUC bisa kokarinta na kafa sabbin jami’o’i a Najeriya, musamman yadda a baya-bayan nan da akasarin sabbin jami’o’i da hukumar ta ba wa lasisi a yankin Arewa suke.

A ranar Litinin Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da ba da lasisi ga wasu sabbin jami’o masu zaman kansu guda 37 kuma yawancinsu a Arewaci suke

Adamu ya ce an kaddamar da sabon manhajar karatun jami’o’in ne domin tabbatar da ilimin jami’o’i a Najeriya ya dace da zamani.

Don haka ya yi kira da a yi duk mai yiwuwa wajen sama musu wadatattun kayan aiki domin cimma wannan hadafi.

Ya kuma yi kira da a kafa hukumar kula da aikin koyarwa domin inganta harkar ilimi.

Da yake nasa jawabin, Shugaban NUC, ya ce a halin yanzu jami’o’i 148 masu zaman kansu ne a Najeriya kuma 87 (kashi 60%) daga ciki an kafa su ne a zamanin Minista Adamu Adamu.