Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita.
Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka canza fiye da kima, ta hanyar ba su wuta daidai da abin da suka ƙware su.
NERC ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki ya zama dole saboda kamfanonin sun yi kunnen ƙashi bayan umarnin da ta ba su, wanda ya ƙayyade kuɗin da su caji kwastomomi da ba su da mita.
Ta ce waɗanda aka ci tarar sun haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) da Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC), Kamfanin Rarraba Lantarki na Jos da kuma Kamfanin Rarraba Lantarki na Yola.
- ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja
- NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya
Sauran su ne Kamfanin Rarraba Lantarki na Legas da takwarorinsa na Enugu da kuma Ikeja.
Sanarwar da Hukumar NERC ta fitar ta ce wannan tarar ta shafi kamfanonin guda takwas ne daga watan Yuli zuwa Satumbar shekarar 2024.
Ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna kamfanonin sun yi watsi da umarnin nata da ya ƙayyade cazar kwastomomi marasa mita da ke kan layin lantarki guda a duk wata.