Wata mata mai shekara 43 ta gurfana a gaban kotu bisa zargin ta da cin zarafin wani dan sanda ta hanyar gantsara mata cizo.
’Yan sanda na tuhumar matar da neman tayar da zaune-tsaye ta hanyar ta kai wa Insfekta Edoh Ogiri hari da kuma cizon sa, a lokacin da yake kokarin shawo kan mutanen da ke bin layin shiga banki a Jihar Ogun.
- Kisan Ummita: Yau za a ci ga da shari’ar Dan China
- Jirgin kasa ya yi awon gaba da motar ma’aikata a Legas
Mai gabatar da kara, E.O. Adaraloye, ya shaida wa kotun cewa wadda ake tuhuma ta aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Maris da misalin karfe 1:30 na rana a bankin Polaris da ke garin Ota.
Ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 249 (d) da 356 na kundin laifuffuka na Jihar Ogun na 2006, sai dai wadda ake tuhumar ta musanta aikata laifin.
Alkalin kotun, Misis A.O.Adeyemi, ta bayar da belin wadda ake kara a kan kudi N250,000 da kuma gabatar da mutum daya da zai tsaya mata.
Sannan dole ne wanda zai tsaya mata ya kasance mazaunin yankin da kotun take tare kuma ya gabatar da shaidar biyan haraji ga gwamnatin Ogun.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Maris.