Adadin gawarwakin da aka gano bayan nutsewar wani kwalekwalen fasinja a Jihar Neja ya karu zuwa bakwai.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar (NSEMA) ta ce an gano karin gawarwaki uku daga cikin fasinjoji 24 da kwalekwalen ke nutse da su.
- DAGA LARABA: Me Ya Sa Waɗanda Suka Kammala Jami’a Ke Komawa Sana’ar Girke-Girke?
- Yadda mace za ta yi amfani da Corset wajen ado
A ranar Litinin da dare jirign ya nutse da fasinjojin a hanyarsu ta zuwa Karamar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi daga kauyen Agwara da ke jihar Neja, sai ranar Talata da yamma masu aikin ceto suka gano gawarwakin.
Shugaban Hukumar NSEMA, Garba Salihu ya shaida wa wakilinmu a ranar Laraba cewa wadadanda aka gano gawarwakin nasu da suka hada da ’yan Jihar Neja mutum biyar da kuma kuma Kabawa biyu.
Shugaban hukumar ya ce ana ci gabada aikin ceto domin gano sauran wadanda iftila’in ya ritsa da su.