✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar Mokwa – Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin Neja

Gwamnatin jihar Neja ta ce har yanzu akwai sama da mutum 700 da suka bace ba gan sub a tun bayan ambaliyar ruwan da aka…

Gwamnatin jihar Neja ta ce har yanzu akwai sama da mutum 700 da suka bace ba gan su ba tun bayan mummunar ambaliyar ruwan da aka yi a karamar hukumar Mokwa da ke jihar.

Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi babban dogarin tsohon Shugaban Kasa marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayin ziyarar jaje kan ambaliyar a Minna ranar Talata.

Gwamnan, wanda mataimakinsa, Yakubu Garba ya wakilta ya kuma ce akalla mutum 207 ne aka tabbatar da mutuwarsu sannan gidaje sama da 3,000 ne suka rushe.

“Sama da mutum 700 ne suka bace kuma ba a san inda suke ba. Wannan ambaliyar ta jawo mana babbar asara,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa hukumomi da kamfanoni da ma daidaikun jama’a da suka ba da tallafi, inda ya ce iftila’in annoba ce ta kasa baki daya.

Gwamnan ya kuma ce yanzu haka gwamnatin na dakon sakamakon binciken hukumomi kan musabbabin ambaliyar da hanyoyin kauce mata a nan gaba.

Tun da farko, Al-Mustapha ya ce ya je jihar ne domin jajanta mata kan mummunar ambaliyar ta Mokwa

“Za mu gana da masu rike da sarautun gargajiya da musamman Ciyaman din karamar hukumar ta Mokwa domin mu yi musu addu’ar kare faruwar hakan a nan gaba,” in ji shi.

Ya kuma ce tawagar jajen tasu ta kunshi muhimman mutane daga sassa daban-daban na kasar nan domin jajantawa da bayar da tallafi ga gwamnati da yankunan da ta shafa.