✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8

Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da…

Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’.

A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa.

Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai Rubutu da ta zanta da Aminiya ta wayar tarho, ta ce an tsinci gawar a kan hanyar da ruwa ke wucewa.

“Gawar wani babban mutum ne, amma ba za mu iya gane shi ba saboda tuni ya fara lalacewa. An binne shi a wurin tun da ba a iya motsa gawar,” in ji shi.

An yi ƙoƙarin jin ta bakin Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, domin ƙarin bayani lamarin ya ci tura.

Tun da farko hukumar ta tabbatar da mutuwar mutane 161, yayin da wasu da dama suka ɓace bayan iftila’in ambaliyar.