✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mace za ta yi amfani da Corset wajen ado

Ana amfani da corset ta yadda ainihin siffarta za ta fito, tare da boye taiba da kuma turo kirjinta tare dai fito da siffar kugunta.

Asalin corset kayan adon matan turawa ne a karni na 19, inda suke amfani dahi wajen fito da siffar halittarta.

Ana amfani da shi ne wajen matse ciki da hakarkarin mace, ta yadda za ta fito a siffar V, tare da mikar da cikinta da boye taiba da kuma turo kirjinta tare dai fito da siffar kugunta.

Mata na ci gaba da amfani da shi a wannan zamani a matsayin muhimmin abu wajen kawata kwalliyarsu musamman a lokacin bukukuwa.

Amare da yawa suna amfani da shi a rigarsu ta fitar biki, haka ma kawayen amarya, sukan yi amfani da corset saboda sanin muhimmancinta da kuma yadda ado da ita ke burgewa.

Don haka Aminiya ta kawo maku hanyoyin da za ku bi wajen amfani da kwalliyar corset musamman ga amare ko da sauran mata.

Akwai hanyoyi da hudu da ake sanya corset kamar haka:

  • Ana daurawa a jiki sannan a sanya riga a kanta.
  • Ana dinka ta a cikin riga.
  • Ana dinkawa a saman riga
  • Ana daurawa a saman rigar da aka sanya.

Sai dai kuma corset ba kayan kwalliya ba ne da ake sanyawa ba da rigar zaman gida ko ta shan iska.

Yadda ake amfani da Corset

Na farko kuma mafi muhimmanci shi ne ki samu corset da ya dace da yanayin jikinki. Kar ki sake ki yi amfani da wanda ya matse ki sosai, ballantana ya yana lo nufashi da kyau. Ki tabbatar ya yi daidai da jikinku.

Wasu sukan bayyana corset dinsu, inda suke dinkawa a saman rigansu, a matsayin ado.

Wasu kuma suna dinka ta ne ta cikin rigarsu ta yadda idan suka sa rigar, za ta yi musu cif-cif, ba tare an ga alamar corset din ba. Shi ya wata sai kin lura sosai kafin ki gane cewa tana sanye da shi.

Idan kika yin dace samun corset daidai da jikinki, to zai taimaka wajen sanya kayan su yi miki cif-cif kamar a jikinki aka dinka.

Tsayuwarki za ta kasance a mike babu doro ko lankwasa ko tattara, sannan uwa uba, zai fito da shape dinki da kyau, kuma ya boye tumbi.

Ki tabbatar da cewa kayan da za ki dinka corset a kansu na kure adaka ne, ba na zaman gida ba, domin kuwa kwalliyar corset ta fi dacewa da kayan zuwa taro ko kuma biki.