✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da lakcara saboda sa dalibai gwale-gwale a Kano

Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano ta dakatar a wani malaminta kan wahalar da dalibai.

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano ta dakatar a wani malaminta kan sa dalibai gwale-gwale.

Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar, Sa’idu Nayaya, ya sanar a ranar Laraba cewa an dakatar da malamin ne sakamakon wani bidiyonsa da ya karade kafofin yada labarai.

 A cikin bidiyon an ga malamin yana sa dalibai gwale-gwale a cikin aji saboda sun makara, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce da kiraye-kirayen neman taka masa burki. 

“Hakan ne ya sa aka dakatar da shi nan take aka mika lamarin ga kwamitin ladabtarwa na manyan malamai domin daukar matakin da ya dace.

“Hakan zai tabbatar da adalci da kuma hana sake faruwar irin haka a nan gaba.”