✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke barauniyar dan firamare a Kwara

Kotu ta tsare matar da ake zargi da satar dan makabartar firamare a a gidan gidan yari

Dubun wata mata da ake zargi da sace wani karamin yaro a wata makarantar firamare ta cika a garin Ilori, Jihar Kwara.

An cafke matar mai shekara 29 ne  bayan ta yi awon gaba da wani dan firamare a kofar shiga makarantar da ke unguwar Gamno a garin na Ilori.

Ganin ta tsere da yaron ne aka bi ta a guje, inda wani mai babur ya yi nasarar cafko ta tare da yaron ta yi yunkurin sacewa.

“Da aka kalubalance ta sai ta ikirarin cewa ita ce mahaifiyar yaron,” a cewar mai gabatar da kara, Gbenga Ayeni, a lokacin da ake gurfanar da wadda ake zargin a gaban kuliya.

Bayan sauraron karar, alkalin kotun majistaren, Monisola Gbadeyan Kamson, ta ba da umarnin tsare matar a gidan yari, sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba da muke ciki.