Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kogi ta ce ta bankado ma’aikatan bogi 268 da ke karbar albashi a matsayin ma’aikatan Babbar Kotun jihar.
Shugaban Kwamitin Tantance Ma’aikatan, Mai shari’a Mohammed Etsu Umar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a lokacin da yake gabatar da rahoton ga Mukaddashin Alkalin Alkalai, Mai shari’a Josiah Joe Majebi, a Lokoja babban birnin jihar.
Kwamitin ya kuma ba da shawarar a dakatar da duk wasu nade-naden mukamai ba bisa ka’ida ba a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kogi a tsakanin watan Janairu 2021 zuwa Yuni 2022.
Mai shari’a Umar, ya ce rashin sanin ya kamata ya haifar da karuwar ma’aikata bogi wadanda ba a gani a fili, wanda hakan ke nuna karin kashi 40 cikin 100 na kudaden ma’aikata.
“Bayan an yi nazari sosai kan sunayen sababbin ma’aikatan da aka dauka daga Janairu 2021 zuwa Yuni 2022, jadawalin sunayen ma’aikatan da kuma lissafin albashinsu, an gano cewa ba a iya samun wasu sunayen halastattun da ke cikin jerin sunayen ma’aikatan na kotunan da sauran reshen ma’aikatar.
“Saboda haka, alamu ne da ke nuna cewa, duk da sunayensu na cikin takardar biyan albashi, ba su da wuraren aiki kuma ba sa aiki a ko’ina a ofisoshin Ma’aikatar,” in ji shi.
A cikin jawabinsa, Mukaddashin Alkalin Alkalai ya ce, zai kasance yana ci gaba da aiki don tabbatar da bin tsari da kuma himma wajen daukar ma’aikata da gudanarwa.
Ya yi alkawarin aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya gabatar ba tare da bata lokaci ba.