✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta kashe fiye da mutum 200 a Congo

Sakataren MDD, Antonio Guterres, ya jajanta wa wadanda ibtila’in ya auku a kansu.

Alkaluman mamatan da aka samu sanadiyyar ambaliyar ruwa a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo sun kai 203 ya zuwa yanzu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumomin Gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun bayyana cewa, adadain mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar laka ya kai 176.

Gwamnan Lardin Kudancin Kivu ya ce, har yanzu akwai dimbin mutanen da suka bace da ba a ji duriyarsu ba kuma ana fargabar laka ta binne su.

Ambaliyar ruwan ta shanye akalla kauyuka biyu da suka hada da Bushushu da Nyamukubi masu makwabtka da Tafkin Kivu a yankin na gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo.

Kazalika an samu mummunar zabtarewar laka wadda ta lalata gidajen katako da aka yi musu rufi da karafa.

Kafafen yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa, fiye da kashi daya bisa uku na daukacin gidajen yankin, duk ruwa ya yi awon gaba su da suka hada da cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu.

Ibtila’in ya auku ne kwanaki biyu bayan an samu asarar rayukan mutane 131 a Rwanda, tsallaken Tafkin na Kivu sakamakon ambaliyar ruwan da zabtarewar lakar.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya jajanta wa wadanda ibtila’in ya auku a kansu sanadiyyar mummunar ambaliyar ruwa a Rwanda da Congo