✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madatsar Ruwan Lagdo na yi wa jihohi 3 na Nijeriya barazanar ambaliya

An fara aikin wayar da kan jama’a sakamakon ƙaruwar saukar ruwan sama da ake samu a ’yan kwanakin nan.

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna wasu jihohin Nijeriya uku na cikin shirin ko-ta-kwana, sakamakon ƙaruwar fargabar samun ambaliya saboda yiyuwar sakin ruwan Madatsar Lagdo ta Kamaru.

A cewar wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, jihohin da mazauna ke cikin zaman ɗar-ɗar sun haɗar da Benuwe da Edo da kuma Bayelsa, waɗanda tuni suka fara shiri don kauce wa barazanar ambaliyar.

Sai dai Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Nijeriya ta yi watsi da rahotonnin da ke cewa an buɗe madatsar ruwan, a yayin da tuni jihohin suka fara shirya wa barazanar.

Gwamnatin Benuwe ta ce ta fara aikin wayar da kan jama’a sakamakon ƙaruwar saukar ruwan sama da ake samu a ’yan kwanakin nan.

Jami’ar yaɗa labarai na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Benuwe, Tema Ager ta ce a yanzu haka suna jiran umarni daga ma’aikatar albarkatun ruwa ta ƙasar.

Sai dai ta ce Ministan Albarkatun Ruwan, Farfesa Joseph Utsev, ya yi watsi da rahotanni da ke cewa Gwamnatin Kamaru fara sako ruwa daga Madatsar Ruwan na Lagdo.

Aminiya ta ruwaito cewa, kusan duk shekara dai Gwamnatin Tarayya takan shawarci al’ummomi da ke yankuna a sahun gaba-gaba da su dauki matakan da suka dace domin dakile illar da ka iya haifar da ambaliyar ruwa saboda bude Madatsar Ruwa ta Lagdo.

Da ma duk shekara sai hukumomin Jamhuriyar Kamaru sun saki ruwan Madatsar Lagdo saboda tumbatsar da take yi, abin da kan janyo mummunar ambaliyar ruwa da ke shafar wasu jihohin Najeriya.