A ranar Lahadin makon jiya ne Najeriya ta shiga bi sawu sauran kasashen duniya wajen Bikin Ranar Abinci ta Duniya.
Bikin ya zo ne a daidai lokacin da mutanen kasar nan suke fuskantar barazana da fargabar samun karancin abinci a badi saboda yadda ambaliya ta yi matukar barnata gonaki da dama.
- Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya zama dan gudun hijira
- Ku shirya wa matsananciyar yunwa a Arewa —Sarkin Zazzau
Aminiya ta ruwaito zuwa farkon makon nan, ambaliyar ta bana ta kashe akalla mutum 603, sannan ta shafi akalla mutum miliyan 1.4 a jihohi 33 da Babban Birnin Tarayya Abuja daga cikin jihohi 36 na kasar nan.
Haka kuma Aminiya ta ruwaito cewa ambaliyar ta lalata akalla hekta dubu 146 da 734 na gonaki a fadin kasar nan, inda ta fi yin barna a jihohin da aka yi noma.
Hukumar Kula da Samara da Abinci da Noma na Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta hanyar rahoton Kungiyar Cadre Harmonisé ta kiyasta cewa akalla mutum miliyan 19.4 ne a jihohi 21 da Babban Birnin Tarayya Abuja suke fama da karancin abinci a yanzu haka.
Wannan rahoton na Cadre Harmonisé yana zuwa ne a matsayin wani gargadi da za a iya cewa ya zo a kan lokaci, inda ya nuna fargabar samun karancin abinci, musamman a nan Arewa.
A duk ranar 16 ga Oktoba ce ake yin Bikin Ranar Abinci ta Duniya, inda ake wayar da kan mutanen da suke fama da karancin abinci tare da kiraye-kiraye kan yadda za a samar da wadataccen abinci a duniya.
Da yake jawabi a wajen bikin na bana a Abuja, Ministan Aikin Gona, Dokta Mohammad Mahmood Abubakar ya ce sauye-sauyen yanayi da duniya ke fuskanta na kawo fargabar karancin abinci, inda ya ce Najeriya na yin duk mai yiwuwa wajen fuskantar matsalar.
“Muna yin kokarinmu domin ganin mutanen Najeriya ba su shiga tsananin yunwa ba.
“Wannan ya sa muka adana hatsi a ma’adananmu a garuruwa daban-daban, inda muke da kusan tan dubu 100.
“Idan ba ku manta ba, a lokacin annobar COVID-19, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin mu rabar da tan dubu 70, wanda ba karamin.
Taimako ya yi ba
Wannan shi ne matakin da kasashe suke dauka domin fuskantar barazanar yunwa.
“Don haka ina tabbatar muku cewa muna da shirye-shirye masu kyau da muke yi domin tabbatar da cewa ’yan Najeriya ba su shiga yunwa ba.
“Mun san matsalar tsaro ta shafi harkokin nomanmu, amma ba ma fama da karancin abinci a yanzu, kuma za mu yi duk abin da za mu iya domin hana faruwar haka,” inji Ministan.
Sai dai duk da tabbacin da Ministan ya bayar, masu ruwa-da-tsaki a bangaren noma da sauran jama’a sun ce dole sai gwamnatin ta kara kaimi.
Manoma sun yi asara
Manoma a fadin kasar suna kukan cewa ambaliya ta barnata musu gonakinsu, inda a cewarsu ta janyo musu asarar miliyoyin Naira.
Manoma a yankin kogunan Neja da Binuwai sun yi asarar mai yawan gaske, inda ambaliyar ta fi shafar manoman shinkafa da masara, wanda hakan ya sa ake fargabar samun karancin abincin kasancewar hatsi biyu da aka fi bukatar ne ambaliyar ta fi shafa.
Kabiru Ibrahim, Shugaban Gamayyar Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) ya ce, “Ranar Abinci ta Duniya ta bana ta zo wa Najeriya a daidai lokacin da muke fama da matsalolin tsaro da ambaliya da suke matukar shafar harkokin noma da kuma fargabar kawo hauhawar farashin kayayyakin abinci.”
A cewarsa, idan har ana so a dakatar da yiwuwar samun karancin abinci, “Dole mu koma gona, musamman wuraren da ambaliyar ta fi barna, mu yi amfani da fasahar zamani wajen sake noma gonakin da rani.”
Za a samu tsada da karancin abinci – Manoma
Aminiya ta zanta da wasu manoma, inda da yawansu suka ce yadda suka yi fama da tsadar taki da sauran kayan noma, sannan ambaliya ta zo ta lalata gonakin hakan na almanta yiwuwar karancin abinci da tsadarsa a kakar bana.
Alhaji Dallatu Muhammad, shi ne Sarkin Noman Karamar Hukumar Gujba, yankin da ya samu ambaliyar ruwa mai yawan gaske, ya ce, “Babu shakka za a fuskanci karancin abinci da tsadarsa domin kamar ni a yanzu haka akwai gonar da nake noma buhu 100 na dawa amma a bana ban yi tsammani zan samu buhu 20 ba saboda ambaliyar.
“Ko a yanzu ma farashin buhun gero daya bai gaza Naira dubu 18 ba, maimakon a ce yanzu tunda kakarsa ce a ce buhu kada ya wuce Naira dubu 12 ko 13.
“Haka bayan ambaliyar sai ga masifar tsadar takin zamani, inda buhun NPK ya kai Naira dubu 25.
“Ke nan ga tsadar taki, ga shi kuma amfanin bai yi kyau ba saboda ambaliya, ai ka ga lamarin sai addu’a,” in ji shi.
Shi kuwa Alhaji Auwalu Abdullahi manomi a Karamar Hukumar Damaturu ya ce, “Ba a cewa komai domin kuwa duk da wahalar rayuwa da al’umma ke fuskanta da tunanin za a samu saukin farashin abinci, sai dai Allah Ya kawo mana dauki, saboda tun yanzu alamomi na nuna sai taimakon Allah kawai.”
Don haka ya roki gwamnatocin jihohi da ta Tarayya su kawo dauki ga manoma lura da asarar da suka yi, sannan ya ce gwamnati ta kai dauki ga al’umma musamman na kayayyakin abinci don rage matsalolin tsadar abincin da za a iya fuskanta.
A nasa bangaren, Alhaji Ibrahim March da ke Karamar Hukumar Jakusko a Jihar Yobe ya ce, har zuwa yanzu mafi yawan gonakinsu suna cikin ruwa tsundum ta yadda sai dai wani ikon Allah su da samun amfanin gona.
Ya ce gonar da yake samun dawa buhu 80, a bana da kyar ya samu buhu 10.
Haka gonar da yake samun buhu 300 na shinkafa a bana da wuya ya samu buhu 20 domin mafi yawan shinkafar ambaliya ta tafi da ita.
Alhaji Bala Faru, manomi ne kuma tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa ta Jihar Sakkwato, ya ce ambaliyar a halin da ake ciki da kyar za a iya samun rabin abin da aka zata na amfanin gona bayan ta rashin wata hanya da ambaliya ta yanke ta a hanyar Jakusko zuwa Gashuwa, wanda hakan ya sa a cewarsa, “Wajibi farashin abinci ya daga sosai.”
Matsalar tsaro
Ya ce bara shinkafa samfarera ta shiga kasuwa a Naira dubu 15, amma a bana, farashin da ta shiga kasuwa shi ne Naira dubu 22.
Ya ce masu kamfani sun ki bari kananan ’yan kasuwa su saya, “Muna da kananan masana’antu amma ba mu ganin shinkafar gaba daya, don haka dole mun bar aiki saboda tsadar shinkafar da gas, ga kasuwannin kauye ba a iya zuwa saboda matsalar tsaro.
“Za a samu karancin abinci sosai.
“A bara buhun shinkafa mai toliya ya shigo kasuwa kan Naira dubu 28, amma ya kai Naira dubu 55.
“A bara buhun gero ya shigo a Naira dubu 16, yanzu Naira dubu 22, masara a bara Naira dubu 12 yanzu Naira dubu 20,” in ji Alhaji Bala.
Aliyu Labaran ya ce yadda ambaliyar ta lalata gonakin da suka noma, kasancewar rashin tsaro ya sa ba a yi noman ba sosai, dole za a samu karancin abinci.
Ya ce dan kadan din da aka samu kuma, zai yi tsada sosai.
Tuni dai jama’a suke kuka kan tsadar kayan abinci kafin faruwar ambaliyar da ake ganin za ta dada tabarbara al’amura tare da barazanar haifar da yunwa a badi, idan aka yi la’akari da talauci da tsadar abinci da ake ciki da kuma wanda za a fuskanta a badi.
Daga: Isiyaku Muhammed da Nasiru Bello, Sakkwato da Isah Hussaini, Jos da Sani Saleh Chinade, Damaturu.