✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen da suka mutu a ambaliyar Neja sun ƙaru zuwa 88 —NSEMA

Gwamnatin jihar ta ce akwai yiwuwar yawan mutanen da suka rasu a ambaliyar zai ƙaru

Yawan mutanen da suka rasu a sakamakon mummunar ambaliyar ruwan sama a yankin Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ya ƙaru zuwa 88.

Shugaban Sashen Ayyuka na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Husseini Isah, ne ya sanar da haka a ranar Juma’a.

Ya ce, “adadin mamatan na ci gaba da ƙaruwa, amma a halin yanzu mun ƙirga mutum 88.” Hussain Ya ƙara da cewa ana ci gaba aikin ceto.

Aminiya ta ruwaito cewa wasu mutum 12 ’yan gida ɗaya suna cikin mutanen da ambaliyar ta yi ajalinsu.

Ambaliyar ta yi rusa da gidaje sama da 50 tare da sanye murare da dama.

Tun da farko kakakin Hukumar NSEMA, Ibrahim Audu Husseini, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “akwai yiwuwar yawan mutanen da suka mutu da sauran asarar da aka yi za su ƙaru, saboda akwai masu aikin ceto a wurare daban-daban.”