Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Gombe ta sanar da 3 ga watan Yuni a matsayin ranar fara jigilar maniyyatan jihar domin sauke farali a Kasar Saudiyya.
Sakataren hukumar a jihar ta Gombe, Alhaji Sa’adu Hassan, ya shaida wa manema labarai jihar ta samu kujeru 2,556 cikin kujeru aikin Hajji 95,000 da aka bai wa Najeriya.
Ya kuma yaba wa maniyatan bisa yadda suke halartar bita domin koyon yadda za su gudanar da aikin Hajji.
Dangane da masauki a Kasa Mai Tsarki kuwa, ya ce Hukumar Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta samar musu da masauƙai masu kyau a kusa da Harami.
- Buhari ya yi bakin kokarinsa, ya kamata ya huta —Garba Shehu
- Shugaban karamar hukuma ya rasu ana dab da rantsar da shi a Yobe
Haka kuma an samar da isassun jami’ai da za su jagoranci maniyatan jihar wajen gudanar da aikin Hajjin cikin nasara.
Sakataren hukumar ya shaida wa manema labarai cewa Hukumar NAHCON ta umurce su da su sanar da maniyatan na bana cewa rikicin ƙasar Sudan, ne ya jawo wannan kari domin za a canja hanyar da aka saba bi ba ta sararin samaniyar kasar Sudan.
“Ya zama dole mu karkata ta wasu ƙasashe kafin zuwa Saudiyya, Wanda hakan zai ɗauki ƙarin sa’o’i saboda zagayen” inji shi.
A cewarsa wanann zagayen ne ya jawo wa kowanne maniyyaci ƙarin Dala 250, amma daga cikin kudin Gwamnatin Tarayya ta biya wa kowannenau Dala 150, shi Kuma maniyaci zai bia sauran Dala 100.
Sa’adu Hassan, ya ce maimakon a nemi kowanne maniyyaci ya kawo ƙarin kudin, sai hukumar NAHCON ta yanke shawarar cirar kuɗin daga cikin kuɗin guzurinsu, don haka, maimakon a bai wa kowa Dala 800 yanzu Dala 700 za a ba su.