✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi bakin kokarinsa, ya kamata ya huta —Garba Shehu

Garba Shehu ya ce lokacin ya yi da Buhari zai koma gida ya huta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci hutu bayan shekaru takwas a yana jagorantar Najeriya, a cewar mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Garba Shehu.

Hadimin na Buhari ya bayyana haka ne a tashar talabijin ta Channels, inda ya ce “Babu wata kasa a duniya da ta magance dukkan matsalolinta dari bisa dari.

“Amma Shugaban Buhari ya yi bakin kokarinsa a kasar nan, don haka ya cancanci ya koma gida ya huta, kuma ’yan Najeriya su girmama shi bayan haka,” in ji shi a ranar Alhamis.

Garba Shehu ya ce Buhari ya sha fama da suka da bakaken maganganu daga ’yan Najeriya, amma haka bai sa ya gaza ci gaba da yi musu kabakin romon dimokuradiyya ba.

“Za a rika tunawa da Obasanjo a harkar sadarwa, za a rika tunawa da Shagari wajen hada kan kasa, kuma ’yan Najeriya za su tuna da Buhari da yadda ya kara karfin wutar lantarki zuwa megawatt 20,000 da kammala Gadar Neja ta biyu da biyan fansho da yin gadoji,” in ji shi.

“Ba mu taba ganin aiki irin wanda Buhari ya yi a duk tarihin Najeriya ba; Yara miliyan hudu ne ba sa zuwa makaranta, amma yanzu sun koma makaranta.”

Sai dai ya koka cewa ’yan Najeriya na kin nuna godiya ga gwamnatin Buhari, ko da yake, “Yawanci sai shugabanni sun bar mulki ake fara yabo da kaunar su.

“ Gwamnati mai zuwa za ta dora daga inda Shugaba Buhari ya tsaya,” in ji Garba Shehu.