✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan bai wa ‘yan Najeriya kunya ba —Tinubu

Tinubu ya ce ya shirya wa aikin da ke gabansa na saita Najeriya.

Shugaban Kasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan Najeriya tabbacin cewar ba zai ba su kunya ba.

Tinubu ya bayyana haka ne bayan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari mai barin gado ya karrama shi da lambar girmamawa ta kasa mafi daraja (GCFR) a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Alhamis.

Ya ce ya fahimci ma’anar karramawar da aikin da ke gabansa, inda ya yi alkawarin ba zai bai wa ’yan kasar kunya ba.

“Ni mutum ne mai saukin kai wanda ke cin gajiyar goyon baya da fatan al’ummar Najeriya. Jama’a sun dogara gare mu. Ka yi aikinka ya mai girma shugaban kasa.

“Yanzu wannan babban nauyi ya hau kaina. Na fahimci ma’anar girmamawar da aka ba ni a yau da kuma aikin da ke jira na.

“Dole ne na gudanar da aikin da ke gabana da kyau. Matsalar tsaro, tattalin arziki, noma, guraben ayyuka, ilimi, lafiya da wutar lantarki da sauran bangarori dole ne mu tashi tsaye a ka su. Wannan nauyi da ya hau kaina ba zan ba ka kunya ba, mai girma shugaban kasa.”

Ya gode wa Buhari bisa karrama shi da ya yi da kuma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda aka ba wa lambar GCON.

Ya kara da cewa sadaukarwar da shugaban kasa ke yi na samar da kyakkyawan shugabanci da dimokuradiyya ba abu ne mai sauki ba.

Tinubu ya kuma yaba wa shugaba Buhari bisa karrama marigayi MKO Abiola, wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka soke a ranar 12 ga watan Yunin 1993.

“Daya daga cikin abu mafi girma da aka yi, shi ne amincewa da rashin adalcin da aka yi na soke zaben 1993, sannan aka sanya watan Yuni a matsayin ranar dimokuradiyya, da kuma bai wa marigayi MKO Abiola babbar lambar karramawa.

“Cikin hikima aka waiwayi tarihi sannan aka yi abin da ya dace, tare da sanyaya zukatan wadanda aka bata wa.”

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya.