✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ke hana ’yan Arewa cin gajiyar siyasa a Kudu

Dan Masanin Ibadan ya bayyana dalilan da suka hana ’yan Arewa samun romon dimokuradiyya.

Alhaji Yahaya Ali, Dan Masanin Ibadan shi ne tsohon Mai ba Gwamnan Jihar Oyo Shawara a kan Al’amuran ’Yan Arewa mazauna Jihar da aka fara nadawa a wannan mukami.

A hirarsa da Aminiya ya bayyana dalilan da suka hana ’yan Arewa samun romon dimokuradiyya a Kudu musamman jihar duk da cewa sun shekara sama da 100 a can:

Wane ci gaba kake gani ’yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yamma sun samu a shekara 25 na mulkin dimokuradiyyar Nijeriya?

Idan ka lura za ka gane cewa tun kafin 1999, ’yan Arewa mazauna Jihar Oyo mun samu dama masu yawa wadanda suka kamata mu yi amfani da su wajen ci gabanmu a fannin siyasa.

Amma sai wasu shugabannin Hausawa da suka samu kusantar gwamnati suka sa son zuciya wanda hakan ya haifar da subucewar irin wadannan damarmaki a wancan zamani.

Misali, Gwamnan farar hula na farko a Jam’iyar UPN a 1979 zuwa 1983, marigayi Cif Bola Ige ya samar da tsarin daukar nauyin karatu na fiye da yara 100 a manyan makarantu na ciki da wajen kasar nan ga dalibai ’yan asalin Jihar Oyo.

Amma Hausawa da suka shafe sama da shekara 100 a jihar ba su samu gurbin ko dalibi daya ba, saboda son zuciya na Hausawan da ke cikin gwamnati a wancan zamani.

Sun boye wadannan bayanai tare kin isar da sakon ga mutanenmu.

Mu kuma a wancan zamani da kuruciyarmu muna cikin makaranta ba mu kai matsayin kusantar mahukunta ba, balle mu iya fafutikar kwato hakkin mutanenmu.

Irin wannan tafiya aka rika yi tun da Nijeriya ta samu ’yanci har zuwa shekarar 2015 da Gwamna Abiola Ajimobi ya lashe zabe a Jam’iyar APC, inda ya nada ni a matsayin Bahaushe na farko Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin ’Yan Arewa a Jihar.

Kana ganin nadin naka ya yi tasiri ga mutanenka a mulkin dimokuradiyyar?

Kwarai kuwa domin fafutikar neman hakkinmu da muka fara ce ta kai mu ga samun wannan matsayi Hausawa suka fara cin romon dimukuradiyya yanzu a Jihar Oyo.

Shi ma Gwamna Seyi Makinde na Jam’iyar PDP ya bi wannan salo inda ya nada Bahaushe da ke rike da wannan matsayi a yanzu.

Shi ke nan abin da ’yan Arewa ke bukata a gwamnatin Jihar Oyo?

Ko kusa ba za mu tsaya a nan ba, yanzu haka akwai kwamitin amintattu a karkashin jagorancina da zai lalubo hanyar dinke barakar da ake samu a tsakanin shugabannin ’yan Arewa magoya bayan jam’iyyu a jihar.

Muna so mu kai ga matsayin samun kujerar kwamishina da ta Majalisar Dokokin Jihar da ta tarayya.

Hakan zai iya samuwa idan muka yi nasarar hada kan al’ummarmu domin tafiya da murya daya.

Makwabciyarmu Jihar Legas ta nada Bahaushe a matsayin kwamishina ya shafe shekara 8 yana aiki.

Haka wasu jihohin Arewa sun nada wasu kabilun Yarbawa a matsayin kwamishinoni.

Tunda haka ne me zai hana mu yi fafutikar samun irin wannan matsayi a Jihar Oyo, musamman saboda akwai mutanenmu da suka cancanci samun wannan matsayi?

Wace cancanta Hausawa suka yi domin samun irin wannan matsayi a siyasance?

Na farko dadewarmu zaune a wannan sashe. Na biyu shi ne irin gudunmawar da mutanenmu suke bayarwa a fannin kasuwanci da ke bunkasa tattalin arzikin jihar.

Sai na uku a bangaren ilimin zamani akwai daruruwan ’ya’yan Hausawa da suke da digiri na daya da na biyu da na uku. Sun yi karatu a ciki da wajen jihar har da kasashen waje.

Sai muhimmin abu na hudu shi ne siyasa, inda yanzu haka muna cikin manyan jam’iyyun da suke fafatawa a Jihar Oyo, ba mu bari an bar mu a baya ba. Wadannan abubuwa 4 sun ishe mu fafutikar neman karin mukamai.

Kamar yadda na fada tun farko babbar matsalarmu ita ce rashin hadin kanmu don tafiya da murya daya.

Amma idan Allah Ya yarda kwamitin amintattun zai yi aikin da zai kai mu ga cim ma wannan buri a nan gaba.

Ba ka ganin matsalar kabilanci da ake nuna wa ’yan Arewa a wannan sashe zai iya hana kwamitin yin aiki?

Na yarda kabilancin da ake nuna wa ’yan uwa a wannan sashe yana iya yin tasiri wajen kawo wa kwamitin cikas.

Amma idan ka lura da yadda gwamnonin baya da suka hada da Sanata Rasheed Ladoja da marigayi Otunba Christopher Alao Akala da marigayi Sanata Abiola Ajimobi suka janyo mu a jiki a zamanin mulkinsu, wannan ya isa hujjar nuna sun yi kokarin tafiya da mu a cikin gwamnati amma aka samu matsalar son zuciya daga bangaren mu Hausawa.

Wane kira za ka yi ga ’yan Arewa mazauna jihar a kan ci gabansu?

Ina rokon daukacin ’yan uwa da muke zaune a Jihar Oyo mu ci-gaba da hakurin da muka saba yi a baya wajen kyautata zamantakewarmu da jama’ar gari kuma abokan zama wato Yarbawa a cikin kasuwanni da sauran wuraren zama.

Kuma mu girmama doka da oda domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakaninmu da su. Yin haka zai kai mu ga cim ma burinmu da kuma ci gabanmu ta fannin tafiya tare da mutanenmu a gwamnatoci masu zuwa.

Sannan ina kira ga sarakunan Hausawa da shugabannin kungiyoyin ’yan Arewa duk lokacin da kwamitin amintattun ya fara aiki su yi wa Allah da Annabi su ba kwamitin hadin kai da goyon baya a taimaka wajen samun nasara.

Idan muka yi hakuri muka yafe wa juna, to a nan gaba ’ya’ya da jikokinmu za su taso su girbi abin da muka shuka masu na alheri.