Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya ƙaddamar da kashi na biyu na shirin tallafa wa mata, inda ya ware miliyan Naira 260 domin tallafa wa mata 5,200 a faɗin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar.
Yayin wani biki da aka yi a gidan gwamnatin jihar, Abba ya raba tsabar kudi Naira 50,000 ga duk mace, da nufin rage wahalhalun tattalin arziƙi da inganta rayuwarsu.
- Yadda aka yi wa yarinya fyaɗe a ofishin ’yan sanda a Legas
- Shekara 100 a duniya: Sheikh Dahiru Bauchi ya sake kafa tarihi
Abba ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ke ware Naira miliyan 260 a kowane wata domin shirin, wanda wani ɓangare ne na tallafa wa matasa da mata, da kuma rage basussukan fansho.
Ya kuma ƙarfafa wa gwiwa matan da su yi amfani da kuɗaɗen cikin hikima wajen inganta tattalin arziƙinsu da kuma rage raɗaɗin talauci.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin yin tsafta, musamman a wannan lokaci na damina, don tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya.
Ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin ilimi, kiwon lafiya, da koyar da sana’o’i, inda ya yi nuni da cewa tsarin na inganta rayuwa a Jihar Kano.
Sugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Hashimu Dungurawa, ya yaba da shirin, inda ya ce wani muhimmin mataki ne na rage wa mata raɗaɗin halin da ake ciki.
Ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamna Yusuf na cika alƙawuran da ya ɗauma a lokacin yaƙin neman zaɓensa don inganta rayuwar mazauna Jihar Kano.