Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallami Kwamishinan Filaye da Safiyo na gwamnatin jihar, Adamu Aliyu Kibiya daga muƙaminsa.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan Labarai na Kano, Baba Halilu Ɗantiye ya fitar a daren nan.
- Gwamnatin Sojin Nijar ta soke fasfon jami’an gwamnatin Bazoum
- Tinubu zai tafi Amurka taron Majalisar Dinkin Duniya
Lamarin dai na zuwa ne bayan an zargi Adamu Kibiya da furta kalaman tunzura al’umma da ke nuna rashin da’a da mahukuntan shari’a.
A yayin da ake dakon shari’ar kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Kano da aka gudanar a watan Maris, a bayan nan an naɗo Kibiya yana barazanar kisa ga duk alkalin da ake zargi da karbar na goro.
Aminiya ta ruwaito cewa, sallamar ta kuma shafi mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin wasanni da matasa, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye wanda shi ma ake zargi da furta kalaman da ba su dace ba a madadin gwamnatin.
Bayanai sun ce Ogan Boye ya yi kalamai na tunzura al’umma da ake zargin cin zarafi ne ga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.
A ƙarshen makon nan ne bidiyon jami’an gwamnatin suka riƙa yawo a shafukan sada zumunta, inda suke furta kalamai wanda Gwamnatin Kanon ta ce ba za ta lamunta ba daga kowane jami’in gwamnati.
A cikin wata sanarwa da Baba Ɗantiye ya fitar, ya ce jami’an gwamnatin sun yi magana ba tare da izinin gwamna ba.
Baba Ɗantiye ya ce gwamnan ya gargadi duk wani jami’in gwamnati kan kada ya sake katsalandan kan abin da bai shafi hurumin ma’aikatarsa ba.
Ana iya tuna cewa, a baya dai ɗaya daga cikin alƙalan kotun ta yi zargin cewa akwai wasu da ke yunƙurin bai wa alƙalai da lauyoyin kudi.