✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Sojin Nijar ta soke fasfon jami’an gwamnatin Bazoum

Daga cikin waɗanda lamarin ya shafa akwai ’yan Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma Libya da Turkiyya.

Gwamnatin Sojin Nijar ta soke fasfunan tafiye-tafiye na jami’an hamɓararriyar gwamnatin Mohamed Bazoum.

Bayanai sun ce an soke fasfon sama da jami’ai 990 da suka haɗa da ’yan ƙasar da kuma ’yan ƙasashen ƙetare da suke da alaƙa da gwamnatin.

Wannan dai na ƙunshe ne a cikin wani saƙo da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar ɗin ta wallafa a shafukan sada zumunta.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da manyan jami’an hukumomi da cibiyoyi da tsoffin daraktoci da masu bayar da shawara ga hamɓarren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum.

Daga cikin waɗanda lamarin ya shafa akwai ’yan Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma Libya da Turkiyya da wasu daga cikin ƙasashen Yammacin Afirka 50.

A ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata ne sojoji suka hamɓarrar da gwamnatin shugaba Mohammad Bazoum, kuma ana ci gaba da yi masa ɗaurin talala a gidansa.

A ƙarshen watan Agustan da ya gabata, sojojin sun soke fasfunan jami’an gwamnatin da dama waɗanda ke a ƙasashen waje da suka haɗa da firaminista da ministan harkokin wajen da kuma Ambasada Nijar a Faransa.