Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta shiga sarkakiya bayan ta amince za ta sakin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum da matarsa Khadija.
Majiyoyi da dama a Najeriya da makwabciyarta Nijar, sun tabbatar da shirin gwamnatin mulkin soja na sakin hambararren shugaban kasar a cikin ‘yan kwanaki na watan Ramadan.
- Fim ɗin ‘Oppenheimer’ ya kafa tarihi a bikin ba da lambar yabo na Oscars
- Mutum fiye da 500 sun warke daga cutar Sanƙarau a Yobe
Sai dai an gano cewa babban abin da ya jefa manyan jami’an soji a Jamhuriyar Nijar cikin rudani shi ne nacewar da Bazoum ya yi na ci gaba da zama a cikin kasar ta Nijar, bisa dalilin cewa ba ya sha’awar komawa wata kasa.
Majiyoyin da suka zanta da Aminiya kan shirin sakin Bazoum sun hada da jami’an diflomasiyya da ‘yan jarida.
Wasu mazauna birnin Yamai, babban birnin kasar, da kuma Maradi daya daga cikin manyan biranen kasar, sun ce wata fitacciyar jarida a kasar cikin harshen Faransanci ta ambato labarin shirin sojojin na sakin Bazoum.
Majiyoyin sun ce hukumomin sojin na aiki kan yadda “abubuwa za su tafi daidai”, idan har suka bar Bazoum ya ci gaba da zama a Jamhuriyar Nijar.
Wani bangare na fargabar gwamnatin mulkin sojin shi ne yiwuwar samun zanga-zanga daga masu goyon bayan hambararren shugaban kasar domin neman a ba shi cikakken ‘yanci, tun da yarjejeniyar a halin yanzu ita ce Bazoum zai gaba da kasancewa a cikin wani tsari na daurin talalar zaman gida ba fita.
Jaridar Niger tabloid De L’enqueteur ta nakalto wasu majiyoyi masu inganci na cewa “za a sauya tsarewar da aka yi wa Bazoum da matarsa zuwa daurin talala na zaman gida ba fita nan da kowane lokaci kafin shigowar watan Ramadan.”
Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Yulin bara ne Bazoum da matarsa da kuma dansa, Salem suke tsare a hannun sojojin da suka yi juyin mulki.
Sai dai a ranar 9 ga watan Janairun da ya gabata ne wata kotun ta bayar da umarnin sakin dan Bazoum na wucin gadi.
Daya daga cikin majiyar ta ce babu sa hannun Faransa ko ECOWAS a cikin wannan yunkuri na sakin hambararren shugaban.
Haka kuma majiyar ta ce yunkuri sakin Bazoum mataki na cikin gida, ma’ana an shirya hakan kuma an amince da shi a cikin Nijar.
Wata majiyar kuma ta ce Bazoum a nasa ra’ayin ya bayyana muradinsa na ci gaba da zama a Nijar bayan an sake shi, wanda hakan ya tabbatar da kishin kasar duk da dambarwar siyasa da ta wakana.
“Saboda haka a kan wannan mas’alar ce sojojin ke tababar, domin su a nasu raayin za su fi samun nutsuwa idan Bazoum zai ketare ya bar kasar ya tafi wani wuri,” in ji daya daga cikin majiyoyin.
“Suna laakari ne da farin jininsa duk da cewa sun tabbatar wa ‘yan kasa cewa su masu kishin kasa ne kuma ba su dora wa kowa karan tsana ba.
“Duk da cewa ba sa adawa da sakin hambararren shugaban, abu daya a bayyane yake, ba sa son dawo da shi kan karagar mulki.