✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fim ɗin ‘Oppenheimer’ ya kafa tarihi a bikin ba da lambar yabo na Oscars

Fim ɗin ‘Oppenheimer’ ne aka fi zaɓa a wannan shekarar, wanda ya mamaye lambobin yabo 7.

Fim ɗin Oppenheimer da aka yi kan tarihin yadda aka fara ƙirƙiro makaman nukiliya da ake kira Atomic Bomb shi ne ya kafa tarihin lashe kyautuka bakwai a rukuni daban-daban yayin bikin ba da lambar yabo na Oscars a bana.

Jarumin Hollywood, Cillian Murphy wanda ya fito daga yankin Ireland a Birtaniya, shi ya haska a matsayin Julius Robert Oppenheimer, mutumin da Turance ake yi wa laƙani da Father of Atomic Bomb.

An dai soma bikin Oscars na 2024 da Da’Vine Joy Randolph, wadda ta lashe lambar yabo ta farko a daren wadda dama an yi hasashen za ta samu lambar yabon.

A ranar Lahadi 10 ga watan Maris ne aka yi bikin karrama wasu fitattun ’yan wasan fina-finai da suka taka rawar gani da lambar yabon Oscars ta shekarar 2024.

Da’Vine Joy Randolph, na daga cikin waɗanda suka lashe lambar yabon Oscars a shekarar 2024 a daren Lahadi, nasarar da aka yi ta hasashe a kai.

Fim ɗin ‘Oppenheimer’ ne aka fi zaɓa a wannan shekarar, wanda ya mamaye 7 daga cikin rukunoni 13 da ya yi takarar da su, ciki har da Mafi Kyawun Hoto da Babban Darakta.

Haka kuma, jarumin fim ɗin,  Cillian Murphy, ya lashe kyautar jarumin fina finan da ya fi kowa fice a shekarar da ta gabata, a wajen bikin karrama gwarzayen Oscar na bana.

Cillian Murphy, ya doke Paul Giamatti, Bradley Cooper, Jeffrey Wright da Colman Domingo.

A rukunin fitaccen fim mai ba da labari na kasa-da-kasa, an zabi fim ɗin “I.O Capitano,” wanda mai ba da umarnin nan dan kasar Italiya Matteo Garrone ya haɗa, a takarar lashe lambar yabon, sai dai “The Zone of Interest” na kasar Birtaniya ne ya lashe wannan rukunin.

Fim ɗin na ‘I.O Capitano’ ya bibiyi labarin wani karamin yaro ne, wanda ya bi ayarin baƙin haure daga Senegal ya ratsa ta hamada a Nijar zuwa Libya, inda suka shiga wani kwale-kwalen ’yan fasa-kwauri da ke maƙare da baƙin haure.

Ga dai jerin wasu da suka yi nasara a bikin gasar Oscars ta ranar Lahadi:

Fim mafi fice/Mafi Kyawun Hoto

“Oppenheimer”

Jaruma

Emma Stone da ta fito a fim ɗin “Poor Things”

Jarumi

Cillian Murphy, “Oppenheimer”

Kyautar wanda ya fi taimaka wa jarumin shiri

Robert Downey Jr., “Oppenheimer”

Babban Darekta

Christopher Nolan, “Oppenheimer”

Gyara Hoto da Bidiyo

“Oppenheimer,” Jennifer Lame

Tsara Hoto da Bidiyo

“Oppenheimer,” Hoyte Van Hoytema

Fim na Ƙasa da Ƙasa

“The Zone of Interest” (United Kingdom)