Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa a matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu.
A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci ta hanyar yin adalci.
- Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe
- Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa
“Mutumin nan Abacha—kullum sukarsa da cin amanarsa kuke yi a asirce. Tarihi zai tuna ka a matsayin shugaba nagari, ko da kuwa sun ci gaba da ƙoƙarin rage maka ƙima.
“A matsayina na ɗanka, yau na fi alfahari da kai. Lallai kai ne mutumin da suke so sun zama ko da rabinka ne kuwa,” in ji shi.
Ya kammala rubutunsa da karin maganar Hausawa: “Duk wanda ya yi jifa a kasuwa…”
Rubutun nasa ya zo ne kwanaki kaɗan bayan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya ƙaddamar da littafinsa.
Littafin ya jawo cece-kuce sosai, musamman kan soke zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993.
A cikin littafin, Babangida ya tabbatar da cewar MKO Abiola ne ya lashe zaɓen, amma ya ce wasu a cikin gwamnatinsa, musamman Abacha, suka tilasta masa soke sakamakon zaɓen.
Janar Sani Abacha ya mulki Najeriya daga 1993 zuwa lokacin rasuwarsa a 1998.
Wasu na yaba wa mulkinsa saboda gyaran tattalin arziƙi da tsaro, yayin da wasu ke sukarsa bisa cin hanci da take hakkin ɗan Adam.
A gefe guda kuma, Gumsu Abacha, ɗaya daga cikin ’ya’yan marigayin, ta mayar martani game da littafin da IBB ya ƙaddamar.
A wani saƙo gajere da ta wallafa a shafin X (Twitter), wanda ke kama da habaici.
Haka kuma, ta sake wallafa wasu rubuce-rubuce da ke cewa Babangida ya zargi Abacha da laifuka ne domin ba shi da ikon kare kansa.
Ga hotunan a ƙasa: