Gwamnatin Kano ta kaddamar da rabon kayan tallafi domin rage wa al’ummar jihar radadin cire tallafin man fetur.
Kimanin buhunan abinci masu nauyin kilo goma-goma guda dubu dari 457 wanda ya hada da masara buhu dubu 160 da shinkafa buhu dubu 297 gwamnatin ta tanada don raba wa al’ummar jihar.
- Ukraine: Rasha ta sanya makaminta na kare-dangi cikin shirin ko-ta-kwana
- Tinubu na nazarin shigar da Najeriya ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arzikin duniya
Aminiya ta ruwaito cewa an kaddamar da rabon tallafin kayan abinci da kuma jari na kayayyakin noma ranar Litinin a Ofishin Hukumar Bunkasa Ayyukan Noma ta Jihar (KNARDA).
Ana iya tuna cewa, Gwamnatin Tarayya ce dai ta ba jihohin kasar nan tallafin Naira biliyan biyar biyar don raba wa al’ummarsu a wani mataki na rage radadin janye tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.
Da yake jawabi, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa tana sane da halin da al’umma jihar ke ciki na yunwa da talauci da kuma rashin sana’ar dogaro da kai.
“Muna sane da halin da al’ummar jiharmu ke ciki don haka muke kokari wajen lalubo hanyoyin da za a rage musu radadi.
“Muna roko da a kara hakuri yanzu aka fara wannan tallafi insha Allah za a ci gaba da tallafa wa al’umma.”
Ya ce tallafin ba wai kawai rage radadin janye tallafin mai zai yi ga mutane ba, a gefe guda kuma tallafin zai magance talauci a tsakanin mata da matasan jihar.
Ya ce tallafin zai fantsama ga mutane da dama tun daga matakin jihar har zuwa kan kananan hukumomi da kuma mazabu a fadin jihar.
Ya kuma ce kimanin mata 2,357 ne za su amfana da tallafin dabbobi da suka hada da awaki da tumaki domin dogaro da kawunansu.
Haka su ma manoma 1,200 za su amfana da kayayyakin noma da suka hada da injinan casa da taki da sauransu.
Daga cikin mutanen da za su amfana da tallafin kamar yadda gwamnan ya bayyana sun hada da gidajen gajiyayyu da gidajen renon yara kanana da masu bukata ta musamman da makarantun Islamiyyoyi da asibitoci da kananan ma’aikatan gwamnati.
A cewar gwamnan, kowacce mazaba daga cikin mazabu 4,084 da ke jihar za a ba su buhun masara 564 da na shinkafa 330.
Ya yi kira ga wadanda za su ci moriyar tallafin da su yi amfani da wannan dama yadda ya kamata.
Gwamnan ya ce don tabbatarwa kayayyakin tallafin sun isa ga wadanda aka yi abin domin su, sun kafa kwamitoci wanda za su tabbatar da yiyuwar lamarin wanda dukkanin kwamitocin na mazabu da kananan hukumomi har zuwa jihar a karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Dokta Bappa Bichi.
Da yake jawabi tun da farko, Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Ayyukan Noma ta Jihar Kano, Dokta Farouk Kurawa, ya bayyana cewa, hukumar za ta raba kimanin buhuna dubu 160 wanda za a raba ga kananan hukumomi hudu da suka hada da Karamar Hukumar Dala da Gwale da Dawakin Kudu da kuma Karamar Hukumar Birni da Kewaye.
Darakta Janar din ya nemi Gwamnatin Jihar da ta kara yawan malaman gona a hukumar duba da yawan manoma da ke fadin jihar.