✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na nazarin shigar da Najeriya ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arzikin duniya

A halin yanzu Afirka ta Kudu ce kaɗai daga Afirka ta samu zama mamba a ƙungiyar ta G-20.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana nazarin aika buƙatarta ta shiga ƙungiyar ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arzikin duniya, ake yi laƙabi da G-20.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ya ce gwamnati na auna alfanu ko kuma kasadar da ke tattare da zama mambar a ƙungiyar.

A ranar Litinin ne Shugaba Bola Tinubu zai tafi birnin Delhi domin halartar taron ƙungiyar bisa gayyata ta musamman da Firaministan Indiya Narendra Modi ya yi masa.

Aminiya ta ruwaito cewa Tinubu zai halarci taron na G20 da za a yi a birnin New Delhi a ranar 9 zuwa 10 ga watan Satumba.

A cewar Ngelale, Tinubu zai halarci taron ne domin jawo hankalin kasashen waje kai tsaye zuwa kasar tare da hada gwiwa da masu zuba jari masu zaman kansu daga sassan duniya don bunkasa ababen more rayuwa a Najeriya.

Ya ce Tinubu zai gabatar da jawabai yayin taron, wanda ya hada da dukkan shugabannin kasashen da ke halarta da sauran manyan masana’antu da ‘yan kasuwa daga sassan duniya.

Mai magana da yawun shugaban kasar, ya ce a gefe guda kuma shugaban zai gana da takwaransa na Brazil Lula da Silva da Silva, da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Schultz, da Firaministan Indiya, Narendra Modi, da Shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol, da wasu wasu tsirarun shugabannin kasashe kan batun taron G20.

Taron ana yin shi duk shekara wanda aka fara tun lokacin da aka kafa shi a shekarar 2008 bayan rikicin kudi na duniya na 1997-1998.

Mambobin G20 sun hada da: Argentina, Australia, Brazil, Canada, China, Faransa, Jamus, Indiya, Indonesia, Italiya, Japan, Jamhuriyar Koriya, Mexico, Rasha, Saudi Arabia, Afirka ta Kudu, Turkiyya, Birtaniya, Amurka, da Tarayyar Turai.

A halin yanzu Afirka ta Kudu ce kaɗai daga Afirka ta samu zama mamba a ƙungiyar ta G-20.

Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da matakai na farfado da tattalin arzikin ƙasar da ƙarfafa zuba jari amma kuma ƙasar na fama da hauhawar farashin kayayyaki da basussuka da rashin ingancin kayayyakin more rayuwa.