Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Makabartar Dakarun Soji ta Kasa da ke Abuja inda ya halarci jana’izar sojoji 17 da aka yi wa kisan gilla a Jihar Delta.
Tinubu wanda ya isa makabartar da misalin karfe 4:10 na Yammacin wannan Larabar ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da Ministan Tsaro, Abubakar Badaru da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.
Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya da suka halarci jana’izar sun hada Abba Kabir Yusuf na Kano, Sheriff Oborevwori na Delta da Usman Ododo na jihar Kogi da Gwamnan Imo Hope Uzodinma sai kuma na Bayelsa, Duoye Diri.
tuni dai rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kammala dukkanin tsare-tsaren gudanar da jana’izar dakarunta 17, da aka yi wa kisan gilla a yankin Okuama da ke Jihar Delta.
Idan dai ba a manta ba, a tsakiyar wannan watan ne wasu ’yan ta’adda suka yi wa sojojin da ke aiki a karkashin bataliya ta 181 kisan gilla, bayan da suka je kwantar da tarzomar wani rikici da aka samu tsakanin al’umomin Okuama da Okoloba a Jihar Delta.
Bayan faruwar lamarin ne Shugaba Tinubu ya bada umarnin gano masu hannu wajen aikata laifin.
Karkashin wannan umarni da shugaba Tinubu ya bayar, rahotanni sun nuna cewa kawo yanzu jami’an soji sun samu nasarar kama wasu da ake zargi da aikata laifin.
Al’umma da dama ne suka tsere daga gidajensu a yankin da lamarin ya faru, bayan da wasu rahotanni suka zargi sojoji da kai harin ramuwar gayya, zargin da tuni rundunar sojojin Najeriya ta musanta.