Rahotanni na cewa an ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata zuwa gobe Talata.
Gwamnatin Nijeriya ce ta sanar da hakan ta bakin Ministan Labarai, Mohammed Idris yayin ganawa da da BBC.
- APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje
- An kashe ubangidan Turji, Kacalla Ɗanbokolo a Zamfara
Ministan ya ce an ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina.
A cewarsa, “akwai ƙa’idoji da Gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar.
“Saboda haka yanzu ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin Gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,” in ji Ministan.
Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya.
Ya ƙara da cewa tuni ofishin jakadancin Nijeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana’izar.
Alhaji Aminu Ɗantata yana burin binne shi a birnin Madina, inda kuma ’yan uwansa suka nemi amincewar hukumomin Saudiyya game da buƙatar kuma ta sahale musu.
Tun da safiyar yau ne tawagogin Gwamnatin Tarayya da na Gwamnatin Kano suka tafi Saudiyyar domin halartar jana’izar da aka shiryi yi a yau Litinin.
Daga cikin tawagogin akwai Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Haka kuma, akwai tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da kuma malamai irinsu Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Dakta Bashir Aliyu.
A ranar Asabar ce dai Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya rasu a birnin Dubai na Hadaɗɗiyar Daular Larabawa.