Al’ummar Jihar Kano sun bayyana cewa rasuwar dattijo kuma babban attajirin ya bar wani babban gibi mai wuyan cikewa, musamman a bangaren ayyukansa na taimakon marasa karfi da gajiyayyu, ba tare da al’akari da wani bambanci ba.
Aminu Dantata ya taimaka wa cibiyoyin ilimi da na gwamnati da ’yan kasuwa da ayyukan addini a lokuta daban-daban, wanda akasari yake barin mutane da ma shugabanni a cikin mamaki.
Na baya-bayan nan shi ne tallafin sama da Naira biliyan 1.5 ga mutanen da mummunar ambaliyar da aka yi a Jihar Borno ta shafa a shekarar 2024.
Idan za a iya tunawa, farkon shekarun 2000, attajirin ya bayar da gudummawar Naira miliyan 250 domin aikin gyaran Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.
- Jana’izar Aminu Ɗantata: Abba da Sarki Sanusi sun tafi Saudiyya
- Tarihi da tasirin rayuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata
A ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Alhaji Aminu Dantata, wanda ke matsayin kaka ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya rasu ne bayan rashin lafiya yana da shekaru 94.
Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar Malaman Jihar Kano, ta gudanar da sallar jana’izar marigayin ba tare da gawar ba a ranar Asabar, a Masallacin Dangi da ke Kundila Kano. Sallar ta samu halartar dubban jama’a da shugabanni daga ciki da wajen Kano.
Hakan kuwa ta faru ne bayan iyalan marigayin sun sanar bayan rasuwarsa cewa ya bar wasiyya cewa a idan Allah Ya dauki rayuwarsa, binne shi a birnin Madina ta Kasar Saudiyya.
A ranar Lahadi, Sakatarensa, Mustapha Junaid, ya sanar cewa hukumomin Kasar Saudiyya sun bayar da izinin kai gawar Alhaji Aminu Dantata kasar domin yin jana’iza da binne shi a Madina, kamar yadda marigayin ya bar wasiyya.
Alhaji Aminu Dantata, wanda ya shahara da taimakon jama’a da ayyukan addini ne, fitaccen dan kasuwa ne a duniya, kuma tsohon dan siyasa kuma ma’aikacin gwamnati.
Tuni manyan shugabannin Nijeriya da na kasashen duniya suka fara yi wa birnin Madina na Kasaa Mai Tsarki tsinke, tare da tawagawar Gwamnatin Tarayya da gwamnoni da sarakunna da manyan malaman Musulunci domin halartar jana’izar.
Tun bayan rasuwar Aminu Dantata shugabanni da ’yan kasuwa da daidaikun jama’a daga bangarori daban-daban suke ta tururuwar yin ta’aziyya tare da bayyana halayensa na gari da irin gudummawar da ya bayar wajen kawo ci gaba da samar da sauki ga rayuwar al’umma.
Ya bar gibi mai wuyar cikewa — Kanawa
Wani mai sana’ar kanikanci a titin Gidan Zoo da ke Kano, Musa Shehu, ya bayyana cewa, ya shafe shekaru yana aiki a garejin da ya kafa a wani fili mai fadin 100 X 100, mallakin marigayin, amma bai taba sani ba sai daga baya.
Ya ce, “bai taba zuaw ya yi min magana ko ya nemi in tashi ko in biya kudin haya ba. Sai dai kawai haraji da nake biya. Babu wanda zai yi maka wannan sai su Dantata.
“Wurare irin haka na nan birjik inda mutane ke samun kudi ba tare da suna biyan ko sisi ba ga iyalan Dantata. Mutum ne mai ba wa mutane kwarin gwiwa su nemi na kansu domin dogaro da kansu.
“Ba mu taba haduwa da shi ba, amma duk da haka muna amfana da shi sosai daga tarin dukiyar da Allah Ya ba shi. Ba don kwarin gwiwar da muke samu daga gare shi ba, watakila da yawancinmu sun shiga wani hali.
“Mutuwarsa babban rashi ne da mutane da dama za su jima ba su manta da shi ba. Za mu ci gaba da yi masa addu’a, Allah Ya rahamshe shi.
“Gaskiya ba mu taba ganin mutum mai taimakon jama’a kamarsa ba. Kuma ni ban taba ganin mutumin da ya bar dukiyarsa domin kowa ya amfana ba, irinsa.”
Abin koyi ga ’yan kasuwa
’Yan kasuwa a bangarori daban-daban sun bayyana irin kwarin gwiwar da suka samu daga Alhaji Aminu Alhassan Dantata da kuma gwgwarmayar rayuwar attajirin.
Alhaji Auduwa Dogo ya bayyana, Alhaji Aminu, “ya taba cewa, ba na shakkar duk wani mai karbar albashi, komai yawan abin da ake biyansa, amma ina tsoron dan tireda mai kasa kaya a gefen haya, saboda akwai yiwuwar zai wuce haka.”
Ya bayyaan cewa wadannan kalamai na Alhaji Aminu Dantata sun ba wa ’yan kasuwa da a yawa, wadanda a yau sun daukaka.
Shahara da tarihin kasuwancin iyalan gidan Dantata da kuma yadda tsawon lokaci suke tafiyar da shi, ya zama abin koyi ga ’yan kasuwa.
Tun zamannin kakanninsu, Alhaji Alhassan Dantata, iyalan suka shahara da kasuwanci, a cikin Najeriya da ma yankin Yammacin Afirka.
A karshe-karshen rayuwar Alhaji Aminu, ya bayar da karfi a fannin taimaka wa harkokin kasuwanci, kuma mutum ne mai sha’awa da kuma yawan yin alheri a asirce.