✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An soma bincike kan zargin mata masu shan jini a Kano

Wannan lamari bai tsaya iya Jihar Kano ba.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta soma gudanar da bincike kan zargin wasu mata masu shiga gidan mutane suna shanye musu jini.

A baya bayan nan a samu wani bidiyo yana yawo da ke nuna ana dukan wasu mata kan zargin cewa ‘yan shan jini ne.

Haka ma akwai wasu hotuna da ake yadawa na wata mata wadda aka kama a Karamar Hukumar Gezawa wadda aka yi zargin ta sha jinin matar gidan.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar ta Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, kan wanna batu, ya ce sun soma bincike a kan lamarin.

Duk da dai bai tabbatar ko karyata faruwar lamarin ba, ya shaida cewa suna gudanar da bincike.

Da aka nemi karin bayani kan ko an kai musu rahotannin faruwar irin wannan batu, sai ya ce “muna gudanar da bincike” kawai.

Wannan lamari dai na zuwa ne yayin da rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta karyata labaran da ake yadawa cewa wasu mata na shiga gidajen jama’a suna shan jininsu.

TRT ta ruwaito Kakakin ‘yan sandan Jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakil yana karyata rahotannin da ake yadawa a soshiyal midiya cewa wasu mutum 20 da ake zargi da maita sun shiga Bauchi kuma suna shan jinin jama’a.

Ya bayar da misali da wata mata da bidiyonta ya karade shafukan sada zumunta wadda aka yi zargin tana maita, yana mai cewa ba haka lamarin yake ba.

“Matar mai suna Siddika, mazauniyar Unguwar Shekal ce, ta je wata unguwa mai suna Bakin Kura a cikin garin Bauchi domin neman sadaka, sai ta fadi saboda yunwa.

“Sai wasu mata da matasa suka fara jifanta da duwatsu, suna mai cewa mayya ce,” in ji SP Wakil.

Ya bayyana cewa bayan sun samu wannan labarin sai Kwamishinan ‘yan sandan Bauchi CP Auwwal Musa Mohammad ya bayar da umarni aka yi gaggawar ceto matar.

“Binciken da muka yi ya nuna matar tana da tabin-hankali amma ba mayya ba ce kuma mun mika ta hannun iyalanta,” in ji shi.

SP Wakil ya bukaci jama’a su daina yada jita-jita ko abin da ba su tabbatar da sahihancinsa ba.

TRT