A wannan Talatar aka rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal mafi ƙarancin shekaru.
Ɗan kishin Afirka mai shekara 44, ba a ƙasar Senegal kaɗai zai zama shugaba mafi ƙarancin shekaru ba, har ma a dukkan Afirka.
Shugabannin Afirka da dama ciki har da na Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, sun halarci bikin rantsar da shi a garin Diamniadio kusa da babban birnin Dakar.
A matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS, shugaba Tinubu ya ce nasarar Bassirou Faye a zaben Senegal, wani ci gaba ne ga kungiyar a kokarinta na samar da zaman lafiya da tsarin mulki, tare da kara dankon zumunci tsakanin kasashe mambobin kungiyar.
Nan gaba kaɗan dai za a a yi bikin miƙa mulki a hukumance tare da Shugaba Macky Sall a fadar shugaban ƙasa da ke Dakar.
Faye na ɗaya daga cikin ’yan siyasar adawa da aka saka daga kurkuku kwanaki 10 kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar a ranar 24 ga Maris.
Ya fita daga gidan yari bayan afuwar da Shugaba Macky Sall ya yi wa wasu fursunonin siyasa.
Ga wasu hotunan Tinubu da Bassirou Faye a yayin bikin rantsuwar.