Hukumomin Saudiyya sun buƙaci al’ummar Musulmi a faɗin ƙasar da su fara duban watan Zhul Hijjah daga gobe Alhamis da yamma, domin tsayar da ranar Babbar Sallah.
Cikin wata sanarwa da Kotun ƙolin kasar ta fitar ta ce, “Idan Juma’a 7 ga watan Yuni ta tabbata ranar farko ta Zhul Hijjah, Babbar Sallah za ta kasance ranar Lahadi 16, ga watan Yuni kenan.”
- Majalisar Dokokin Kaduna ta buƙaci a binciki El-Rufa’i
- Kotu ta yi umarnin isar da sammaci ga Ganduje ta hanyar sadarwa
Kotun ta buƙaci ɗaiɗaikun mutane da za su iya duba sabon watan, da idanuwansu ko kuma da madubin hangen nesa da su je wata cibiya mafi kusa da su domin taimaka musu zuwa ga kotu mafi kusa domin su bayar da bayani idan har sun ga sabon watan.
Kazalika, Majalisar Koli ta Musulunci a Nijeriya NSCIA, ta bukaci daukacin musulmi a fadin kasar da su dukufa wajen neman jinjirin watan na Zhul Hijjah bayan faduwar rana daga gobe Alhamis.
Gobe Alhamis za ta kasance, ranar 29 ga Zhul Qa’dah ta shekarar 1445 bayan Hijrah, wadda za ta yi daidai da 6 ga watan Yunin 2024.
Babbar Sallah dai na kasancewa ne ranar 10 ga watan Zhul Hijjah, wanda shi ne wata na karshe wato na 12 na Hijirar Annabi Muhammad (SAW).