✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi umarnin isar da sammaci ga Ganduje ta hanyar sadarwa

Lauyan Ganduje ya kalubalanci ingancin lauyoyin Gwamnatin Kano a gabab kotu

Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin a sadar da sammaci ga tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da wasu mutane bakwai ta hanyar amfani da kafofin sadarwa.

Tun da farko Gwamnatin Jihar Kano ce ta yi karar tsohon gwamnan gaban kotu bisa tuhume-tuhume takwas kan zargin karɓar cin hanci, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati.

Wadanda ake karar tare da tsohon gwamnan sun hada da matarsa Hafsat, da dansa, Umar, da Abubakar Bawuro da da Jibrilla Muhammad da kuma Kamfanin Lamash Properties Ltd da Kamfanin Safari Textiles Ltd da kuma Kamfanin Lesage General Enterprises..

Gwamnatin Kano ta ce ta tanadi shaidu 15 da za su bayyana a gaban kotu

Lauyoyin masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Zahraddeen Kofar Mata sun gabatar wa kotun rokonsu na sadar da sammaci ga wadanda ake kara ta hanyar sadarwa inda suka nuna cewa duk kokarinsu na bayar da sammaci ga wadanda ake kara ya ci tura.

Sai dai Barista Nuraini Jimoh wanda shi ne lauyan kariya ga wadanda ake kara ya soki rokon masu, inda ya kafa hujja da cewa bai kamata a saurari rokon ba duba da cewa akwai makamancinsa a gaban wata kotun.

Tunda farko a zanan kotun da lauyan masu gabatar da kara Barista Zahraddeen Kofar Mata da Ya’u suka gabatar da kansu a gaban kotun a matsayin masu gabatar da kara, lauyan da ke kare Ganduje da sauran mutane bakwai Barista Nuraini Jimoh ya yi suka inda ya nuna damuwarsu a kan ingancin lauyoyin.

Sai dai Alkalin Kotun Mai sharia Amina Adamu Aliyu ta yanke hukunci cewa masu gabatar da kara su sadar da sammaci ga wadanda ake kara ta hanyar sadarwa.

Ta kuma dage sauraren shariar zuwa ranar 11 ga watan Yuli 2024 don bayar da bayanai a kan dacewa ko rashin dacewar tsayawar lauyoyin a matsayin masu gabatar da kara