Kungiyar Mata Manoma da ke karkashin Kungiyar Masu Kananan Masana’antu ta Kasa reshen Jihar Bauchi, ta bukaci Gwamnatin Jihar da rika tunawa da mata wajen rabon tallafin noma.
Kungiyar ta hannun Ma’aikatar Gona da Raya Karkara bukaci a rika tsara kasafin kudi da zai tabbatar da daidaito wajen samar da tallafin kudin aiwatar da shirin noma na kasa da zai tallafa wa kowane jinsi, ba tare da nuna bambanci tsakanin maza da mata ba don bunkasa noman abinci a kasa.
- Ya auri mata 9 a lokaci guda don nuna musu soyayya
- Camfe-camfe guda 50 da Hausawa suka yi amanna da su
Shugabar Kungiyar ta Jihar Bauchi, Hajiya Marka Abbas ce ta fadi haka a lokacin musayar ra’ayi kan nau’in abinci a duniya mai taken, ‘Samar da abinci mai gina jiki, muhalli da rayuwa,’ wanda Kungiyar Mata ta Fahimta da Shirin Horar da Matasa Sana’o’i suka shirya, tare da hadin gwiwar Kungiyar Mata Manoma da taimakon Kungiyar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa.
Taron wanda aka yi a ofishin Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Bauchi, ya samu halartar masu ruwa-da-tsaki daga kowane fanni kan harkokin manoma.
Hajiya Marka ta ce, a shekarar 2019 Ma’aikatar Gona da Raya Karkara ta Tarayya ta tuntubi kungiyoyi da masu ruwa-da-tsaki kan su bullo da hanyoyin yadda kowane jinsi zai rika amfana da tallafin noma, kuma ya zamo an samu daidaito a tsakanin maza da mata wajen cin moriyar shirin don inganta shirin wadata kasa da abinci.
Ta bukaci Ma’aikatar Kasafin Kudi ta Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa, an bai wa mata dukkan kudaden da ya kamata su samu domin bunkasa harkokin noma a jihar, ta kuma roki gwamnati ta tabbatar da ana samun daidaito a tsakanin maza da mata wajen rabon tallafin noma, ta yadda za a kawar da batutuwan al’ada da addini da ke yi wa shirin tarnaki a wasu lokuta.
Kuma ta roki gwamnati ta bullo da hanyar sabunta dokar mallakar filayen noma ta kuma samar da wani shiri da zai tabbatar da cewa, mata na morar dukkan tallafin da za a kawo da kuma shiga a dama da su kaitsaye kamar takwarorinsu maza.
Kwamishinan Gona na Jihar Bauchi Mista Jidauna Tula ya ce, wannan taro ya zo a kan lokaci saboda yadda manoma suka samu koma-baya wajen noma abinci, saboda matsalolin karancin ruwan sama da sauyin yanayi da cutar Coronavirus da sauransu.
Kwamishinan wanda Babban Sakatare a Ma’aikatar Alhaji Yakubu Jibril Abdullahi ya wakilta ya gode wa kokarin kungiyoyin mata manoma, sai ya nanata kudirin gwamnati na goya musu baya, sannan ya ce shirin zai taimaka wajen bai wa matan damar tattauna yadda za su bullo da abin da zai taimaka wajen bunkasa noman abinci a kasar nan.
Shugabar Kungiyar Fahimta Hajiya Maryam Garba ta gode wa Ma’aikatar Gona, saboda yadda take tallafa wa kungiyoyin mata manoma da matasa da kudade da kuma horar da su sababbin dabarun noman abinci.