Shugaban Kwamitin Tsaro da Bayanan Sirri na Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya bukaci a binciki rawar da sarankuna ke takawa wajen karuwar matsalar saro a yankunansu.
Da yake bayani a kan ayyukan ’yan fashin daji a mazabarsa ta Sokoto Gabas, Sanata Gobir ya zargi wasu masu rike da sarauta da hannu a hare-haren da ake kaiwa a yankunan.
“Na yarda cewa wasu sarakunan yankin na da laifi. A binciki kowane mai rike da saraura, musamman a yankunan da ‘yan bindiga ke kai hare-hare.
“Gwamnati ta bincika ko suna da hannu kuma ta hukunta masu laifi a cikinsu, domin ba zai yiwu a ci gaba da ganin laifin gwamnati kadai ba.
“Gwamnati tana iya kokarinta amma wasu na yi mata kafar ungulu, don haka ya kamata a gano su wane ne”, inji shi.
Ya Shaida wan ‘yan jarida cewa ba ya goyon bayan sulhun gwamnti da ‘yan bindiga.
“Za ka iya sulhu da masu neman ballewa daga kasa saboda suna neman a kyautata rayuwar mutanensu ne. Amma su wadannan mutane suke kashewa haka kawai”, inji shi.
Ya ce bai taba tunanin za a samu irin wadannan kashe-kashe ba jihar Soktoto da aka “sani da addini da kyawawan dabi’iu”.
“Me ya sa a Arewa kadai abin ke faruwa? Wannan abun da ya kamata a zauna a bincika ne”, inji shi.
Dan Majalisar ya bayyana fargabar cewar kashe-kashen na iya haifar da karancin abinci a saboda manoma na tsoron zuwa gonakinsu.
Ya ce har yanzu Majalisar na kan bakarta na neman Shugaba Buhari ya sallami Manyan Hafsoshi tsaro saboda, “Muna son ganin Najeriya inda kowa ke cikin aminci; inda mutane za su iya zuwa Abuja ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba kuma su isa lafiya”.
Ya yaba da nasarorin da sojoji suka samu a yaki da ‘yan bindiga, sannan ya bukace su da su kara kokari.
“Zan iya cewa yanzu abun ya fi yadda yake a watanni biyu da suka wuce, saboda a watannin da suka wuce lamarin ya kazance fiye da yadda ake tunani”, inji shi.