An kama wani ɗalibi ɗan shekara 20 bisa zargin kashe wata abokiyar karatunsa, ya yanke al’aurarya a Jami’ar Tarayya da ke Lokoja.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kogi, SP William Ovie Aya, ya ce dukkansu daliban jami’ar ne a shekarar farko.
Ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda ana gudanar da cikakken bincike don gano gaskiya game da kisan dalibar mai suna
Aminiya ta gano cewa wadda ake zargin ya yi garkuwa da Damilola tare da cire mata al’aurarta.
- Ambaliya: Dangote ya ba da tallafin N1.5bn a Maiduguri
- Sojoji sun kashe ubangidan Bello Turji a Zamfara
An fara samun labarin bacewar Damilola ne a ranar 4 ga Satumba, 2024 bayan an yi garkuwa da ita a wani dakin kwanan dalibai masu zaman kansu da ke felele Lokoja.
Wanda ya sace ya kai ta wani kwangon gini a yankin sannan ya kira iyalanta ya nemi kudin fansa N400,000, kuma suka biya domin a sako ta.
Da bai gamsu ba, sai ya sake tuntubar su, ya bukaci a kara masa N10m kafin ya sako ta.
Amma ’yan sanda suka bibiya wayarsu har zuwa inda yake, suka kama shi a kokarinsa na karbar kudin fansa N10m.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, amma ya ce shi kaɗai aikata.
Ya kuma jagoranci jami’an tsaro zuwa wani kabari mara zurfi a wani daji a yankin inda ya binne gawar marigayiya Damilola.
A cewarsa, ya kashe ya ne saboda ta ga fuskarsa bayan da ya sace ta.