Soja daya da farar hula huɗu ne ake fargabar sun mutu sakamakon arangama da ɗan sanda a Jihar Nasarawa.
Dan sandan ya caka sa sojan wuka har lahira ne lokacin da ɗan sandan da wani farar hula suke dambe a garin Agyaragu da ke karamar hukumar Obi a jihar.
Wani ganau mai suna Joseph Jonathan ya shaida wa Aminiya cewa, sojan da ya mutu yana kokarin raba fada tsakanin farar hula da ɗan sanda da ke bakin aiki, kuma ana cikin haka ne dan sandan ya daɓa wa sojan wuka har lahira.
A cewar wanda lamarin ya faru a kan idonsa, lokacin da ’yan uwan marigayi sojan suka zo suka ga gawarsa ba rai a kwance, sai suka garzaya ofishin ’yan sanda da ke kusa da wurin suka banka mada wuta.
- Bom ya kashe masu saran ice 7 a Borno
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata A Yi Da Ƙananan Yara Masu Zanga-Zanga
Sai dai ya ce jim kadan bayan an kona ofishin ’yan sanda, rundunar ’yan sandan da ke yaki da garkuwa da mutane ta isa wurin da lamarin ya faru.
Ya kara da cewa, a kokarin kwantar da rikicin, ’yan sanda sun harbe mutum huɗu har lahira.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu ta hanyar sakon murya, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda a jihar, DSP Ranham Nansel ya ce mutane biyu ne kawai suka rasa rayukansu, sauran kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti.
A cewarsa, rundunar ta samu labarin rikicin da misalin karfe 1:00 na rana cewa wani sojan da ke aiki a jihar Borno da ya dawo gida hutu da kuma dan sandan konstabulari sun yi artabu a kasuwar Agyaragu inda sojan ya daba wa ɗan sandan wuka.
Daga nan ɗan sandan ya ƙwace wukar ya daba masa wuka.
“An tabbatar da mutuwar mutane biyu, wasu biyu kuma suna jinya a asibiti.
“Dukansu an garzaya da su asibiti amma sojan ya mutu a lokacin da yake karɓar magani.”
Ya ƙara da cewa, ’yan uwan sojan sun kai farmaki ofishin ’yan sanda, amma jami’an ’yan sandan da ke bakin aiki sun daƙile su.
A cewarsa, kwamishinan ’yan sandan jihar, Umar Shehu-Nadada ya ziyarci wurin da lamarin ya faru domin ganin irin abin da ya yi sanadin mutuwar sojan.
Ya bayyana cewa tun daga lokacin an dawo da zaman lafiya kuma an fara bincike tare da farautar maharan na ofishin ’yan sandan.