Aƙalla ɗalibai 18 na Jami’ar Jihar Kwara, Malete, ne suka tsallake rijiya da baya yayin da motar bas da suke ciki ta kama da wuta a lokacin da suke tafiya.
Ɗaliban sun taso ne daga Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, domin halartar lakcoci a Malete, kwatsam motar bas ɗin mai ɗauke da mutane 18 ta kama wuta a yayin da take ci gaba da tafiya a ranar Laraba.
- Birtaniya za ta rage shekarun masu zaɓe zuwa 16
- RFI ta dauki nauyin buga rigunan Kano Pillars a yarjejeniyar N100m
Lamarin wanda ya haɗa da motar bas mai lamba XUF 134 ZD, ta afku ne a kan hanyar Shao kusa da barikin sojoji na Sobi da misalin ƙarfe 7:54 na safe.
Motar dai ta ƙone gaba ɗaya, amma ba a samu asarar rai ba, yayin da jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara suka isa wurin da lamarin ya faru, inda suka kashe gobarar domin ceto rayukan ɗaliban da za su je harabar jami’ar domin halartar taronsu.
Babban jami’in Kafafen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a madadin Daraktan hukumar, ya ce cikin gaggawar an ɗauki matakin da suka dace kan lamarin kan ceto rayukan mutanen, inda motar bas ɗin ta ƙone ƙurmus.
Adekunle ya ce, “A ranar Laraba, 16 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 07:54, Hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara ta yi gaggawar amsa kiran da aka yi mata game da wata gobarar motar bas mai ɗauke da mutane 18 mai lamba XUF 134 ZD a hanya Shao, kusa da Barrack Sobi.