Wani lamari mai ban al’ajabi ya faru a birnin Lucknow a Jihar Uttar Pradesh da ke kasar Indiya inda wani ya je yin sata amma ya buge da yin barci bayan da ya sha sanyin na’urar AC.
A ranar 2 ga Yuni, 2024 ne wanda ake zargin ya shiga wani gida a yankin Indinagar da niyyar yin satar.
Gidan, mallakin Dokta Sunil Pandey, mazaunin Baranasi, babu kowa a ciki lokacin saboda mai gidan yana bakin aiki.
Barawon mai suna Kapil ya shiga gidan ne ta hanyar bude kofar gidan sannan ya wuce dakin zane, inda ya tarar da na’urar sanyaya daki (AC).
Ya shiga dakin ne a lokacin da ake tsananin zafi sai ya kunna na’urar AC ya kwanta a kasa ya sa matashin kai (filo).
Jin dadin sanyin ya sa barci ya dauki Kapil a karshe ya yi barci mai nisa har gari ya waye masa.
Washegari makwabta suka lura da kofar gidan a bude, kuma sun san cewa gidan ba kowa a ciki.
Bayan sun leka ciki, sai suka gano an tarwatsa gidan, kuma Kapil na barci a cikin minshari. Nan take suka sanar da ’yan sandan yankin.
Jami’ai daga ofishin ’yan sanda na Ghazipur a yankin Indiranagar, karkashin jagorancin SHO Bikas Rai, sun isa gidan don kuma har zuwa lokacin da suka isa yana ci gaba da sharar barci, rike da wayar hannu a hannunsa.
’Yan sandan sun yi yunkurin tada barawon da ke barcin, amma bai farka ba a tashin farko.
Yana farkawa, aka kama shi kuma aka tsare shi a ofishin ’yan sandan yankin kafin a gurfanar da shi a karkashin Sashe na 379 na dokar IPC (manyan laifuffuka).
Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda R Bijay Shankar ya yi tsokaci kan wannan aika-aika, inda ya ce barawon na shaye-shaye ne shi ya janyo masa nauyin barcin.
Da aka sanar da Dokta Pandey batun kutsawar barawon a gidansa, ya nuna kaduwarsa da kuma jin dadin yadda aka kama wanda ya shiga gidan ba tare da lahani ga makwabta ko dukiya ba.
Tuni lamarin ya dauki hankalin mutane, inda jama’ar yankin da dama suka nuna mamakinsu a kan sakarci da wautar barawon.
Kama Kapil ya yi nuni da yadda matsalar sata da tsaro ke ci gaba da faruwa a yankin, lamarin da ya sa jama’a ke tattaunawa a kan bukatar kara sanya ido da inganta matakan tsaro.
Rundunar ’yan sandan ta nanata kudirinta na tabbatar da doka da oda tare da kira ga ’yan kasar su gaggauta kai rahoton duk wani abu da suke zargi.
Wannan lamarin ya zama labari na musamman a cikin jerin labaran aikata laifuffuka a Lucknow, inda haduwar zafi, barasa da na’urar sanyaya daki suka kai ga kama barawon.
Har ila yau, ya nuna muhimmancin wayar da kan jama’a da hada gwiwa da jami’an tsaro don hanawa da kai dauki a duk lokacin da ak ga alamun aikata laifi.
Za a ci gaba da shari’a, inda Kapil zai fuskanci tuhuma kan laifin da ake zargi ya aikata.
Indiya ta tana fuskantar yanayin zafi mai tsanani a tarihi, wanda ya jawo mutuwar akalla mutum 56 da kuma galabaitar kusan mutum 25,000 da ake zargin sun kamu da cutar sankarau saboda zafi daga Maris zuwa Mayun bana.
Tsananin zafin wani bangare ne na sauyin yanayi wanda yanayin zafi ya haura ma’aunin zafi zuwa kusan makin selshiyos 50 a Indiya.
Wannan yanayi mai zafi ne an shafe shekara uku a jere ana irinsa a Indiya, wanda ke nuna karuwar illar sauyin yanayi a nahiyoyin duniya.