✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Zunubai shida ne suka hana Najeriya bunkasa’

Dattijo Nathaniel C.U Okoro, wanda aka fi sani da Nat Okoro shi ne dan kasa na farko da aka nada Manajan Darakta kuma Babban Jami’in…

Dattijo Nathaniel C.U Okoro, wanda aka fi sani da Nat Okoro shi ne dan kasa na farko da aka nada Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC).

Mai shekara 89 a duniya, ba ya son tattauna batun bikin cikar Najeriya shekara 60 da samun ’yanci, saboda inji shi, “Bayan samun ’yancinta, Najeriya cike take da badakala da hassada da kyashi da rudani da yankunan kasar suka haddasa domin su danne junansu.

Okoro wanda zai cika shekara 90 a ranar 26 ga Fabrairun badi, daga bisani ya amince da bukatar Aminiya inda suka tattauna kamar haka:

A ina kake lokacin da aka samun ’yanci a 1960?

Ni ne jami’in lura da zirga-zirga a Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC).

Mene ne tunanin jama’a a wannan rana ta 1 ga Oktoban 1960?

Kana ba ni kunya idan kana magana a kan Najeriya. Wane ’yancin kai kake magana? Shin kana magana ne a kan kafin samun ’yancin kai ko bayan samun ’yancin kai na Najeriya?

Babban abokina dan Ilori ne. Sunansa Laisi Bello, Mahaifinsa mai sarautar gargajiya ne daga garin Uma’ahiya. Umar Aliyu Altine shi ne Magajin Garin Enugu kuma dan Arewa ne. Ba mu san bambanci ba. Wannan ita ce Najeriyar da na sani, ba Najeriyar ’yan siyasar ba-ni-na-iya ba.

Me kake nufi da siyasar ba-ni-na-iya?

Dole ka zama dan siyasar amshin-shata kafin ka ga daidai. Dole ka zama ka san wadansu manya. Mutane kamarmu ba za su taba zama wadansu ba a wannan Najeriya ta yau. Ni ne dan Najeriya na farko da ya rike mukamin Jami’in Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Qasa da kuma Harkokin Cinikayya na Hukumar NRC da ke Kaduna. Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello shi ne ya ba ni na’urar aiki ta farko.

Sardauna bai tava kwana a Kaduna ba a karshen mako koyaushe yana tafiya ne a jirgin kasa. Ni nake tsara dukkan tafiye-tafiyensa. Nakan je in gana da shi. Wata rana ya hadu da ni a shago a Kaduna sai ya tambaye ni, “Me kake yi a nan? Sai na ce masa ina neman na’urar aika sako. Sai ya ce wa mai sayar da kayayyakin ya ba ni, kuma nan take ya biya.

A lokacin yaki na’urar ta bata. Na san sabon Firayi Minista Sa Abubakar Tafawa Balewa sosai, kawuna Raymond Njoku shi ne Ministan Sufuri na farko. Shi ne wanda ya karbi ragamar hukumar daga Tafawa Balewa amma Najeriya ta yanzu ba komai a cikinta sai fanko. Shi ya sa ba ma ci gaba. Allah Ya yi Najeriya a matsayin kasa mai albarka. Najeriya dausayi ne da ke kewaye da hadari kuma kana so in yabe ta, me zan yaba?

Me kake ganin yake tafiya ba daidai ba?

kyashi ya shiga lamarin Najeriya. Najeriya na fama da zunubai shida. Muna fama da zunubin yaudara da rashin dabara da rashin sanin abin da ya kamace mu. Daga ina kake? Muna fama da zunubin hada kai da shaidanu. Na uku muna fama da zunubin hada kai don a yi zalunci.

Wadansu mutane a shirye suke su sayar da iyayensu maza da mata don su samu kudi. Sannan muna fama da zunubin cin amana saboda kishi, ba ka sona, sai ka tafi, ka hada kai da wani domin ka tabbatar ka rusa ni. Kuma akwai zunubin rashin biyayya da cin amana. In har ba mu magance su ba, to babu Najeriya.

Kana nufin wani yanki yana kishin wani?

Haka yake! Dan kabilar Ibo yana jin tsoron kowa amma a shirye yake ya sayar da hajarsa. Kalli Uwalaka, yana nuna ma’aikacinmu mai daukar hoto, idan ka tambaye shi ya sayar da kai, zai sayar da kai saboda kudi. Kabilun Yarabawa maciya amana ne. Yankin Kudu maso Kudu su kuma da su ake hada kai a ci amana. Ba su son dan kabilar Ibo, suna tunanin kabilun Ibo za su danne su saboda haka a shirye suke su yi aiki da Hausawa.

Na yi rubutu mai yawa kan kabilar Ibo. Na rubuta wani abu kan harkokin siyasar bambadanci. Ka san siyasar vangaranci na yi rubutu kan tsartsar vangaranci bisa la’akari da siyasar ko a mutu-ko a yi rai.

Daga furucinka, kana nufin ’yan Arewa suna fada da ’yan Kudu?

Ba haka ba ne amma abin a ciki yake. Shin ka karanta batun hadakar Gwamna Lugard? Ka yi kokari ka samu kwafi, zai fada maka duk yadda lamarin yake. Na farko ba wani abu da ake kira Najeriya. Ba ta taba faruwa ba. Hadin kasa ita ce wacce take da jinsi daya, addini daya, tsari daya al’ada daya. Ba za ka taba kafa kasa mai jinsi biyu ko addini biyu, ba zai taba yuwuwa ba. Wannan shi ne matsalarmu.

Yaya ka samu kanka a Hukumar Jiragen Kasa?

Na gudu ne daga makaranatar sakandare na fara aiki a matsayin Karamin ma’aikaci a mataki bakwai ko takwas ko makamancin haka. Ba na fi kowa kwakwalwa ba ce, na yi aiki tukuru ne. Taken makarantar da na yi ita ce: “Ka yi aiki tukuru, ka yi wasa sosai, Ka tafi dodar.” Ita ce Sakandaren Gwamnati (GSS) da ke garin Oweri. Taken makarantar shi ne ya rika daidaita rayuwata. Da na yi ritaya daga Hukumar NRC a matsayin Manajan Darakta, ba ni da ajiyar Naira dubu biyar a asusuna na banki. A kashin gaskiya ma na gina gidana a kauye ta hanyar matata. A lokacin ma’aikaciyar wucin-gadi ce a Kamfanin Fulawa na Najeriya.

Da ka gudu daga makarantar sakandare ka shiga aiki NRC, shin ka koma ka karasa karatunka?

A’a na yi komai a Hukumar NRC. Na yi makarantar aiki tukuru ne. Na fada maka ina da shaida da dama a kan aikin jiragen qasa.

Ta yaya ka zama Shugaban NRC na farko?

Na sadaukar da yabon ga Janar Muhammadu Buhari wanda shi ne Shugaban Mulkin Soja a wancan lokaci. A wancan lokaci yana ziyarar hukumomin gwamnati da Mataimakinsa. Janar Babatunde Idiagbon. Sun ziyarci Hukumar Tashoshin Ruwa (NPA) a lokacin Bamanga Tukur ne Mukaddashin Janar Manaja. Sun zo Hukumar NRC, sai suka amince da dukkan mu daraktoci shida. Muna Malaga, wani karamin birnin ne da ke kasar Spain, sai muna birnin Landan a ranar Juma’a muka samu labarin cewa Ministan Sufuri yana bukatar ya ganmu a ranar Litinin da karfe 10 na safe. Mun yi tsammanin taro ne da daraktoci suka saba da Minista. Sai muka dawo kuma a ranar Litinin, sai muka tafi kai-tsaye ofishin Babban Sakatare.

Sai Minista ya sanar da mu cewa gwamnati na son ta cike gurbin mukamin Janar Manaja na Hukumar NRC kuma dukkanmu mutum shida mun yi nasara. A hannu daya kuma ni ne Mukaddashin Manajan Darakta. Abin da na fara tunani shi ne in ajiye aiki. Sai kuma wata murya ta gaya mini cewa, “Idan ka yi haka ka taimake su.”

A cikin mutum shida ni kadai ne ba ni da digiri amma ni kadai ne na samu horo na tsawon shekara biyu a fannin injiniya, shekara biyu a fannin injiniyan gyaran inji da shekara uku a harkokin gudanar da aiki da shekara daya a fannin tattali da kididdiga a tsarin harkokin jirgin qasa. Sai zuciyata ta gaya mini cewa ina da matukar muhimmanci. Sai muka zauna jarrabawa. An yi tambayoyi goma kuma an ba mu awa daya.

Godiya ga Allah ina da saurin rubutu kuma da saurin tunani. Yayin da na ga tambayoyin, na san duk amsoshin. Cikin minti 57 na kammala. Muna taronmu na zangon shekara sai aka bayyana mukamina. Minista ya ce, “Ina sanar da ku cewa ina da labari mai kyau da kuma marar kyau ga dukkanku. Labari mai kyau shi ne an zabi daya daga cikinku ya zama Manajan Darakta. Majalisar Koli ta Soja ta amince da nadinka a matasayin Manajan Darakta kuma Babban Jami’i Zartarwa na tsawon shekara daya.”

A gaskiya abin ba komai ne a wurina, saboda ban san za a zabe ni ba. Na farko ni ba dan siyasar bambadanci ba ne, na biyu ni ne mai qarancin takardu. Kowa yana zaton Babatunde za a nada. Ko shi ma yana da kwarin gwiwa. Ya samu matsayi na farko a fannin injiniya amma ya manta ya mayar da hankali ne kan wani fanni na injiniya. Saboda haka ta haka aka cike gurbin mukamin. Buhari ne ya sanya na zama Manajan Darakta.

Bisa bayar da karfi kan takardar shaidar takardu a yau, me hakan ke nuni gare mu a matsayinmu na kasa?

Ba za mu je ko’ina ba. Kamar yadda na gaya maka. Mu kamfanoni biyu ne aka hada mu. Shi (Lord Lugard) ya ba mu shekara 100 mu gwada. Yayin da lokaci ya yi, sai sojoji suka ki su shirya taron tattaunawa. Shi ya sa muke cikin matsala a Najeriya.

Ta yaya za mu kwantar da wannan fargaba mu kuma gyara alakarmu?

Dole ka gyara tunanin mutane da farko. Lokacinmu ya wuce, lokacinka ya wuce. Yanzu dole ka fara tunanin ’ya’yanka don ka sanar da su cewa kai ba Ibo ba ne ko Bahaushe ko Bayarabe. Dole ka zama dan Najeriya. Ba abu ba ne da za a iya yi a rana daya. Abu ne na gaba daya. Ka fara daga makarantu.