Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya ziyarci garin Rann da ke Karamar Hukumar Kala-Balge ta jihar, inda ya rarraba kudaden tallafi ga mabukata da suka rasa iyalansu don su samu damar amfani da kudaden domin yin cefane.
Gwamnan ya ba akalla magidanta 8,000 tallafi, inda kowanensu ya mika musu kudaden a hannunsu saboda babu Bankunan Kasuwanci a yankin.
- Zulum ya damka wa matar hafsan sojin da Boko Haram ta kashe N20m
- Zulum ya gana da iyalan jami’an tsaron da aka kashe a harin Baga
Ya bai wa kowane magidanci N10,000, ya kuma ba mata Naira dubu biyar-biyar da buhun shinkafa daya ga kowanensu.
Gwamnan ya raba kimanin Naira miliyan 65 ga mabukatan da ke Rann tare da tabbatar da an danka musu kudadensu don su samu damar siyan kayan masarufi.
Jama’ar Rann mai makwabtaka da kasar Kamaru, sun gamu da ibtila’in ambaliyar ruwa daga babbar madatsar ruwa da ke Afrika ta Tsakiya, lamarin da tilasta musu hijira zuwa kasar ta Kamaru domin neman matsugunni.
A watannin Yuni da Disamba na shekarar 2019, Zulum ya kai wa al’ummar Rann ziyara, sannan ya sake kai ziyara yankin a cikin watan Fabrairun 2020, inda ya raba wa mutanen da rikici ya ritsa da su kayan abinci da tufafi.